Tuesday, March 17
Shadow

Abin Kunya: Kalli yanda aka bar Gurin da aka warewa Najeriya a taron kasashe dake gudana a Birnin Tokyo na kasar Japan ba kowa, yayin da sauran kasashen Duniya suke tsaye a wajen nasu

Wani dan Najeriya me suna Idris Ayo Bello ya bayyana yanda da ya halarci wajan taron ci gaban Afrika da aka gudanar a birnin Tokyo na kasar Japan da kuma abin kunyar da ya gani.

Yace wajan da aka warewa Najeriya ta tsaya babu kowa a wajan.

Yace da ya ga abin yayi yawa, shine da kansa ya je wajan ya tsaya ya kuma rika amsa tambayoyi akan kasuwancin Najeriya da ci gabanta da wasu ‘yan kasashe ke yi.

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dai ya halarci wajan taron, kuma rahotanni sun bayyana cewa, an tanadi mutanen da zasu tsaya a irin wannan waje dan wakiltar Najeriya.

Karanta Wannan  Mun godewa Allah da kafuwar Jam'iyyar ADC, saboda ta fito mana da bakaken munafukan cikin jam'iyyar mu ta APC wanda suka Munafurci Tinubu a zaben 2023 Karara mun gansu>>Inji Ministan Sufurin Jiragen sama, Festus Keyamo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *