Monday, June 2
Shadow

Abin Kunya:Wata Daya da gama gyaran Matatar Man fetur ta Warri ta sake lalacewa duk da kashe Dala Miliyan $897m wajan gyaranta

Rahotanni sun bayyana cewa, Matatar Man fetur ta Warri da gwamnati ta kashe Dala Miliyan $897m wajan gyaranta ta sake lalacewa.

Rahoton yace ko da aka kammala gyaran, matatar man ta fara aiki a watan Nuwamta na shekarar data gabata ne kuma kaso 40 cikin 100 na matatar ne ke aiki.

Saidai a ranar January 25, 2025 an sake kulle matatar ta daina aiki saboda ta kara lalacewa.

An yi wannan gyaranne a karkashin shugabancin Tsohon shugaban NNPCL, Mele Kolo Kyari wanda tuni ya ajiye aiki.

Wannan lamari yasa ana sukar kamfanin na NNPCL da gazawa.

Karanta Wannan  Buhari ya koma Najeriya bayan gabatar da shaida a kotun Paris

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *