Saturday, November 8
Shadow

Abin Kunya:Wata Daya da gama gyaran Matatar Man fetur ta Warri ta sake lalacewa duk da kashe Dala Miliyan $897m wajan gyaranta

Rahotanni sun bayyana cewa, Matatar Man fetur ta Warri da gwamnati ta kashe Dala Miliyan $897m wajan gyaranta ta sake lalacewa.

Rahoton yace ko da aka kammala gyaran, matatar man ta fara aiki a watan Nuwamta na shekarar data gabata ne kuma kaso 40 cikin 100 na matatar ne ke aiki.

Saidai a ranar January 25, 2025 an sake kulle matatar ta daina aiki saboda ta kara lalacewa.

An yi wannan gyaranne a karkashin shugabancin Tsohon shugaban NNPCL, Mele Kolo Kyari wanda tuni ya ajiye aiki.

Wannan lamari yasa ana sukar kamfanin na NNPCL da gazawa.

Karanta Wannan  ADC TA RIKICI A KEBBI: Shugabanin Jam'iyar ADC A Jihar Kebbi Sun Dakatar Da Ciyaman Engr. Sufiyanu Bala Da Mataimakinsa Junaidu Muhd Da Kuma Sakataren Jam'iyyar Hauwa'u Muhammad

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *