Wednesday, January 15
Shadow

Abincin dake rage kiba

Kuna son rage kiba ta hanyar cin abinci?

Ga abincin dake rage kiba kamar haka:

Kwai

Cin Kwai ta hanyar dafawa ko soyawa a yi Scramble Egg yana taimakawa wajan rage kiba, kuma ba sai an ci da yawa ba.

Yana da sinadaran Kalori wanda basu da yawa amma kuma yana da sinadaran protein da sauransu dake taimakawa daidaita girman jiki.

Gyada, Aya, Gujiya:

Cin Aya, Gyada, Gujiya da danginsu yana taimakawa sosai wajan rage kiba. Suna da sinadarai masu daidaita girman jiki da kuma sawa mutum ya rage kiba wanda basu da illa.

Ganye

Cin ganye irin su zogale, Tafasa, Yadiya, Kabeji, latas,lansir da sauransi na taimakawa matuka wajan rage kiba. Suna da sinadaran rage kiba wanda basu da illa ga lafiya.

Karanta Wannan  Rage tumbi da zogale

Kifi

Kamar dai kwai, Shima kifi yana bayar da sinadaran protein da fats wanda basu da illa kuma suna taimakawa daidaita girman jiki wanda mutum ba zai yi kibar wuce kima ba.

Cin tsaba

Cin abincin tsaba, irin su wake, Masara, Dawa,Gero, Alkama, Shinkafa(ta gida), da sauransu yana taimakawa matuka wajan daidaita jikin mutum.

Cin Tuffa/Apple

Apple ko ace Tuffah na daga cikin ‘ya’yan itatuwan dake da matukar amfani a jikin dan adam, yana da abinda ake cewa Fiber sosai dake hana jiki yin kibar wuce kima.

Wadannan kalar abinci na taimakawa wajan daidai ta jikin mutum,ba zaka rame ba kuma ba zaka yi kibar wuce kima ba.

Karanta Wannan  Rage kiba cikin sati daya

Saidai a runa yana da kyau kada a kama abinci daya cikin wadanda muka lissafa a rika cinshi shi kadai, ya kama idan an ci wannan yau, a ci wancan gobe, idan an ci wannan da safe a ci wancan da rana.

Kuma kada a manta, motsa jiki na da muhimmanci sosai idan ana son daidaita girman jiki. Ba sai ka yi motsa jiki da zai wahalar da kai sosai ba, tafiya kawai da sauri-sauri wadda ake cewa brisk walking a turance ta minti 30 zuwa 60 ta isa a kullun.

Allah ya karemu da lafiya.

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *