Tsohon ɗantakarar mataimakin gwamnan jihar Kano a zaɓen 2023, Murtala Sule Garo ya ce adawar siyasar da ke tsakanin tsofaffin gwamnoni na hana jihar ci gaba.
Garo ya kuma yi kira ga jagororin siyasar jihar su mayar da kubensu, tare da haɗa ƙarfi da ƙarfe domin ciyar da jiharsu gaba.
Garo ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da jaridar Daily Trust ta ruwaito, inda ya ce, “babu daɗi ganin jihohi irin Zamfara da ba ta kai Kano ba, tsofaffin gwamnoninta suna ajiye bambancin siyasa suna haɗuwa domin ciyar da jihar gaba. Mu a nan Kano, da wahala ka samu tsofaffin gwamnoni sun haɗu domin tattauna hanyoyin da za a magance matsalolin jihar.”
“Ina kira ga tsofaffin gwamnoninmu, idan har da gaske suna ƙaunar Kano, su haɗa kai. Ba a samun ci gaba da rabuwar kai. Dole jagororin siyasar jihar su ajiye bambancin siyasa su yi aiki a tare domin ci gaban jihar.”