A matsayinki na matar aure, ya kamata ki rika yiwa mijinki addu’a a gaban idonsa da bayan idonsa.
Misali:
Idan mijinki ya miki kyauta, ki gode masa da fatan Allah ya kawo karin Arziki.
Idan mijinki ya kawo kayan abinci, ya miki dinki, yawa yara dinki ko sayen wani abin farantawa, ya kamata ki masa addu’a a gabansa a bayyane ya ji, hakan zai kara karfafashi da himmatuwa wajan kara yin kamar hakan ko fiye da hakan nan gaba.
Hakanan ki koyawa ‘ya’yanki godiya, idan nahaifinsu ya musu kyauta, su gode masa su kuma yi masa addu’ar budi da kariya:
A yayin da mijinki ya fita nema kuma baya tare dake, yana da kyau ki sakashi a addu’a a yayin da kika yi sallar Walha, da sauran salloli na farilla.
Ki mai fatan kariya daga sharrin mahassada, da sharrin karfe, da sharrin baki, da sauransu:
Hakanan kina iya tashi a karshen dare, misalin karfe 3 ko zuwa 3:30 ki yiwa mijinki addu’a saboda a daidai wannan lokaci Allah yana saukowa kusa da duniya yana amsa addu’ar bayinsa.
Idan kina son yiwa mijinki addu’a ta musamman, kina iya yin Alwala, ki yi sallah raka’a 2, ki yi Istigifari daidai gwargwado, ki yi salatin Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi wasallam) shima daidai gwargwado sai ki daga hanni kiwa mijinki addu’a.
Daga cikin abinda zaki iya fada shine:
Ya Allah ka rufawa mijina asiri ka kara masa budi, kwarin gwiwa da arziki, Ya Allah ya kara masa kaimi wajan kula da ni da ‘ya’yana, Ya Allah ka bashi ikon ciyar damu da halal.
Ya Allah kada ka bar mijina da iyawarsa, ka dafa masa a lamuransa kasa masa Albarkar dukiya, ka saka Albarka a rayuwarsa da tamu ni da ‘ya’yana.
Ya Allah ka kari mijina da lafiya, ka kawar da shi daga dukkan wani abu da zai iya kawar masa da hankali daga hanya madaidaiciya.
Ya Allah ka shiryi mijina hanya madaidaiciya, kasa ya dore akan koyarwar addinin Islama, ka kareshi daga sharrin shedanun mutane da Aljanu.
Allah ka haskakawa mijina wajen nemansa, ka yi masa budi, kasa wannan aiki ko sana’a da yake ta zama sanadiyyar daukakarsa.
Allah ka bamu sa’ar rayuwa ni da mijina da ‘ya’yanmu kasa mu yi dace a Duniya, da Lahira, ka karemu daga kuncin Duniya da Lahira, ka karemu daga tonon Asirin Duniya da Lahira, ka karemu daga jin kunyar Duniya da Lahira, ka rufa mana Asiri, Duniya da Lahira. Kasa mu cika da Imani, ka kare da Azabar Kabari, ka sa mu tashi da imani ranar tashin kiyama, kasa mu samu hisabi me sauki, ka kare mu daga wutar jahannama.
Ya kamata a Rufe addu’a da salati ga Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam).
Idan kuma Mijinki ya riga ya fita, kina son aika masa da sakon Addu’a kina iya aika masa da.
Ina sonka mijina, Allah ya kiyaye hanya ya bada sa’a, ya kareka daga dukkan sharri, ya dawo min da kai lafiya.
Salam Mijina, kamar yanda ka fita da aminci, da farin ciki, da karfin zuciya, Allah ya kaika inda zaka lafiya ya baka sa’ar abinda ka je nema ya dawo min da kai da aminci wanda yafi wanda ka fita dashi, da farin ciki wanda yafi wanda ka fita dashi, da karfin zuciya wanda yafi wanda ka fita dashi.
Mijina Jagorana Allah ya bada sa’a, ya dawo min da kai lafiya.
Mijina ina kewarka, Allah ya bada sa’ar fita ya kawo arziki me amfani.