Saturday, December 13
Shadow

Akwai fargaba da tsoro sosai a zukatan ‘yan Najeriya saboda gazawar jami’an tsaro, da yawan ‘yan Najeriya yanzu su suke baiwa kansu tsaro>>Shugaba Tinubu

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Matsalar tsaro da ta sha kan jami’an tsaron kasarnan ta saka fargaba da tsoro a zukatan mutane.

Yace Manoma na tsoron zuwa gona, ‘yan Kasuwa basu da tabbas akan tsaron rayukansu, sannan mutane an barsu da kare kansu.

Shugaban ya bayyana hakane a Abuja ranar Litinin wajan tattaunawa game da gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya da canja fasalin harkar tsaron kasarnan wanda kwamitin dake kula da canja fasalin kundin tsarin mulkin Najeriya na majalisar tarayya ya shirya.

Shugaban ya bayyana muhimmancin samar da ‘yansandan jihohi wanda yace sune zasu taimaka sosai wajan kare kasarnan.

Karanta Wannan  Rashin kunyarta da rashin bin dokar majalisa ce tasa muka dakatar da ita ba zargin da takewa Sanata Godswill Akpabio ba>>Majalisar Dattijai ta mayarwa da majalisar Dinkin Duniya martani kan dakatar da Sanata Natasha Akpoti

Shugaban ya bayyana hakanne ta bakin ministan Tsaro, Mohammed Abubakar Badaru wanda ya wakilceshi a wajan taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *