Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kammala shiri tsaf dan yiwa majalisar zartarwarsa garambawul inda za’a kirkiro karin wasu ministoci da ma’aikatu.
Daily Trust tace daga cikin sabbin ma’aikatun da ake son kirkirowa akwai ta kula da dabbobi wadda za’a cire daga ma’aikatar noma.
Wannan ma’aikatar ana tunanin zata kawo mafita ga rikicin manoma da makiyaya dake faruwa duk shekara.
Hakanan bayan kirkirar sabbin ma’aikatu ana kuma tunanin shugaban kasan zai samar da kananan ministoci a sauran ma’aikatun da basu dasu.
Masu kula da al’amuran yau da kullun da masu sharhi a harkokin siyasa sun caccaki gwamnatin Tinubu saboda kin saka kananan ministoci a wasu ma’aikatu