Wednesday, January 15
Shadow

Alamomin ciwon ulcer

Menene cutar Ulcer?

Cutar ulcer ko gyambon ciki, kamar yanda aka fi saninta da Hausa, ciwone dake samuwa a cikin dan adam ko kuma a cikin hanjinsa.

Allah ya halicci wata kariya a cikin dan Adam. Kariyarce idan ta samu matsala, sai wasu sinadarai da jikin mutum ke samarwa na sarrafa abinci su ji mada ciwo a ciki ko a hancinsa.

Ana iya maganin cutar ulcer cikin sauki. Amma idan aka barta ba tare da kulawa ba, tanawa mutum illa sosai.

Abubuwan dake kawo cutar ulcer

Abubuwan dake kawo cutar ulcer sun hada da:

  • Cutar da Bakateriya ke sawa.
  • Yawan shan magungunan Aspirin, ibuprofen, da naproxen.
  • A likitance, abinci baya saka ulcer.

Alamomin ciwon Ulcer

Alamar ciwon ulcer ya danganta da tsananin ciwon. Mafi shaharar alamar ciwon ulcer itace jin zafi a tsakanin kirji da ciki. Hakan yafi faruwa idan babu komai a cikin mutum:

Karanta Wannan  Amfanin hakuri a rayuwa

Sauran alamomin cutar ulcer sune:

  • Ciwon ciki
  • Raguwar nauyin jiki
  • Rashin son cin abinci
  • Tashin zuciya da amai
  • Cin abinci kadan a ji an koshi
  • Jin ciwo ko zafi a kirji
  • Jin ciwo yayin cin abinci
  • Jin gajiya da sarkewar numfashi
  • Bakin kashi da ake yi da kyar.
  • Yin amai da jini.

Yawanci ulcer na warkewa cikin sauki idan an yi magani yanda ya dace. A je a ga likita dan tabbatar da cutar da kuma magungunan da suka dace a sha.

Saidai a wasu lokutan da ba kasafai hakan ya cika faruwa ba, ana samun cutar ulcer ta ki warkewa, ko ta rika dawowa akai-akai, ko tasa zubar da jini sosai.

Idan cutar Ulcer ta kai wannan matsayi, kusan sai an yiwa mutum aiki kamin ya warke.

Abincin mai Ulcer

Kamar yanda muka bayyana a sama, a likitance abinci bai saka cutar ulcer ko ya warkar da ita. Amma tunda bacteria ce ke kawo cutar ulcer din, akwai abincin da mutum dake fama da cutar ulcer ya kamata ya rika ci dan kiyaye hakan:

Karanta Wannan  Maganin ciwon gabobin jiki

Abincin mai Ulcer sune:

  • Kabeji da danginsa.
  • Ganye irinsu alayyahu, da ssuransu.
  • Yagwat da danginsa.
  • Tuffa ko Apples.
  • Strawberries da danginsa.
  • Man zaitune.

Maganin Olsa na gargajiya

Idan muka bar bangaren likitanci, a gargajiyance akwai abincin da ake afani dashi wajan taimakawa me ciwom ulcer.

Maganin olsa na gargajiya sun hada da:

  • Probiotic, ana iya amfani da yagwat ko nonon akuya.
  • Zuma.
  • Kaza
  • Kifi
  • Kwai
  • Kabeji

Kada a manta idan an je an ga likita, wadannan abinci ba zasu maye maganin da likita ya bayar ba, a ci gaba da shan maganin likita yayin da ake amfani da wadannan magunguna.

Bagaruwa na maganin ulcer

A likitance dai babu bayanin cewa bagaruwa na maganin cutar ulcer, saidai tabbas ana amfani da ita a gargajiyance wajan maganin ulcer a sassan duniya daban-daban.

Karanta Wannan  Maganin hana karyewar gashi

An ma samu wani bincike da aka yi akanta kan ko tana maganin Ulcer? Kuma ta tabbata cewa lallai tana yi. An yi amfanin da ‘ya’yan danyen bagaruwar ne wajan wannan bincike.

Zogale na maganin Olsa

Tabbas bincike da yawa ya nuna cewa ganyen zogale na maganin ulcer da sauran matsalolin rikicewar ciki.

Kuka na maganin Olsa

Eh. Amma ba kai tsaye ba, a gargajiyance ana amfani da ita, kuma masana sunce tana iya maganin cutar ulcer wadda bata yi tsanani ba.

Yawanci anfi amfani da ‘ya’yan kuka.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *