Friday, July 17
Shadow

Ali Nuhu ya kaiwa gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahya Ziyara inda yace za’a gina cibiyar yin fim a jihar sannan kuma za’a fara koyawa daliban jami’ar jihar gombe yin fim

Tauraron fina-finan Hausa, kuma shugaban hukumar fina-finai ta kasa, Ali Nuhu ya kaiwa Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahya ziyara.

Ali Nuhu yace ziyarar tasa sun tattauna muhimman baututuwa sannan ya samu tarba me kyau.

Ali Nuhu yace daya daga cikin abubuwan da suka tattauna sune naganar gina cibiyar yin fim a jihar Gombe.

Ali Nuhu yace cibiyar zata taimaka wajan karfafa fasaha musamman ta yin fim.

Sannan yace akwai shiri na koyawa daliban jami’ar jihar Gombe yin film.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon da aka ji wasu Kanawa na maganganun da basu dace ba akan shugaba Tinubu yayi da yake saukowa daga jirgi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *