
Tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu kuma shugaban hukumar kula da fina-finai ta kasa ya kaiwa Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ziyara.
Ali Nuhu ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda yace sun yi tattaunawa game da yanda harkar fim zata taimaka wajan inganta tsaro.
