Wednesday, May 28
Shadow

Allah ya min Wahayin mutane 3 da su kadai ne zasu iya kayar da Tinubu zaben 2027>>Inji Malamin Kirista Primate Elijah Ayodele

Babban malamin Kirista, Primate Elijah Ayodele ya bayyana cewa Allah ya masa Wahayin mutane 3 wanda su kadaine idan daya daga cikinsu ya fito takarar shugaban kasa to zai iya kayar da Tinubu.

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan jaridar Tribune.

Yace amma ko da za’a kafa mishi Bindiga ba zai fadi sunayen mutanen ba amma idan dayansu ya fito takara, zai ce Eh Shine.

Yace ko da Atiku ko Peter Obi ne suka ci zabe babu abinda zai canja daga halin da ‘yan Najeriya ke ciki.

Karanta Wannan  Salah ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Premier na bana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *