Monday, December 16
Shadow

Al’umma na tserewa daga ƙauye a Borno saboda barazanar ISWAP

Mayaƙan ISWAP sun bai wa mazauna Kukawa lga sanarwar su bar kauyensu ko kuma su fuskanci kisa kwanaki huɗu da kashe masunta goma sha biyar a yankin Tumbun Rogo.

Wani mazaunin garin da ya gudu daga al’ummarsa zuwa Maiduguri sa’o’i uku da samun wannan barazana, ya bayyana hakan ga gidan talabijin na Channels.

A yayin da ya ke bayar da labarin yadda lamarin yake, mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa mayakan sun tara jama’ar al’umma daban-daban a ƙaramar hukumar da sanyin safiyar Alhamis, inda suka ce su bar gidajensu kafin ranar Asabar, in ba haka ba za a kashe su.

Karanta Wannan  Hukumar 'yansanda tace duk wani dansanda dake hutu ya koma bakin aiki saboda zàngà-zàngàr gobe kuma kada dansandan daya sha giya dan kada yayi tambele a wajan Zàngà-zàngàr

A cewarsa, bayan da suka samu barazanar ‘yan ISWAP din, al’ummomin suka fara barin yankunansu, yayin da wasu suka tafi Kross Kauwa, wasu kuma suka tafi Monguno.

Kukawa lga ƙaramar hukuma ce a gefen tafkin Chadi wadda ta shahara wajen kamun kifi da noma, kuma akwai dakarun sojojin Najeriya da na ruwa.

Duk da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, mayaƙan Boko Haram/ISWAP na ci gaba da kai hare-hare a cikin al’ummomin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *