Wednesday, January 15
Shadow

Amfanin alum a gaban mace

Alum daya daga cikin abubuwan da ake amfani dasu ne wajan tsaftace ruwa da sauran magungunan gargajiya.

Mata na amfani da Alum a shekaru Aruru da suka gabata musamman wajan matse gabansu.

Bari mu duba amfaninsa dalla-dalla.

Amfanin alum a gaban mace

Da yawan mata sukan yi amfani da Alum wajan matse gabansu shekaru aru-aru da suka gabata.

Kuma har a yanzu ma wasu na amfani dashi, saidai a yayin da yake yima wasu aiki, wasu kuwa baya musu aikin yanda ya kamata.

Alum ya kasu kashi-kashi, bari mu duba kowanne da yanda ake amfani dashi.

Alum na Gari a Gaban Mace

Alum na gari farine dake saurin narkewa a cikin ruwa.

Karanta Wannan  Maganin yawan mantuwa

Yanda ake amfani da alum na gari a gaban mace

  • Ana zuba daya bisa hudu na cokalin shan shayi a cikin kofi, sannan a sa ruwa
  • A juya sosai har sai Alum din ya bace.
  • A yi amfani da wannan ruwa a wanke gaban mace a hankali.
  • Bayan an gama a wanke da ruwa me kyau.

Alum na Dutse a gaban mace

Akwai kuma Alum na dutse wanda shima farine ko kuma ace garai-garai wanda ake ganin tsakiyarsa.

Yanda ake amfani da alum na dutse a gaban mace

  • Ana wankeshi da ruwa me tsafta
  • Sannan a gogashi a jikin gaban mace, kada a tura ciki.
  • A wanke da ruwa me tsafta bayan an gama.
Karanta Wannan  Amfanin habbatussauda

Amfanin alum a gaban mace

  • Yana sa gaban mace ya matse.
  • Yana magance cutukan bacteria da kuma hana cutuka shiga gaban mace.
  • Yana taimakawa wajan rage kaikai a gaban mace.
  • Yana hana gaban mace wari.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *