Monday, December 16
Shadow

Amfanin ganyen magarya

Amfanin ganyen magarya

Itaciyar ganyen magarya ana kiranta da Assidir a Larabce. Itaciya ce mai albarka da kuma dimbin tarihi.

Ya kasance ana amfani da ita tun kamin zuwan addinin Musulunci a duniya, bayan zuwan musulunci a duniya sai malamai da wasu magabata masana ilmin tsirran itatuwa suka bada fatawar amfaninta da irin cututtukan da take magani.

Daga bisani suma masana kimiya ba a bar su a bayaba dan sun kaddamar da irin nasu bincike a kan alfanon ganye da kuma diyan magarya. Binciken ya baiwa masana ilimin harhada magani na yankunan turai da wasu yankunan kasahen duniya na Larabawa da India dama nan Afrika wata muhimmiyar damar saka bishiyar magarya a jerin bishiyoyin da ke da karfi da saurin warkar da wasu cututtukka.

Karanta Wannan  Maganin Kaikayin gaban mace

Ga kadan daga cikinsu:

1-Ciwon daji: A dafa garin magarya a misalin kofi daya karami sai a tarfa zuma mai kyau cokali biyu sai a sha da safe bayan an ci abinci. Amma a sanda ake shan magani irin wannan akwai bukatar a kauce wa shan wasu rukunnan magunnan bature.

2-Miki ko kuraje a kan fatar jiki ko wani sashe na gangar jiki: sai a tafasa garin magarya da ruwan khal sai a wanke mikin ko kurjin da kyau da wadannan ruwan sai a marmasa garin magarya kadan a kan mikin bayan ya wuni a haka sai a saka ruwan dumi a wanke maganin sai a sake maimaitawa In sha Allahu za a samu sauki.

3-Cututtukan ciki -kama daga kumburin cikin da baya da alaka da cin wani abinci ko abin sha, zafin ciki da yawan tsuwar hanjin ciki akai akai sanadiyyar wasu kwayoyin cuta na bacteria sai a nemi ganyen magarya mai kyau a sabe sai a saka ruwan dumi a tace da kyau a sha kashi daya daga cikin kashi uku na karamin kofi. Haka za a maimaita da yamma

Karanta Wannan  Amfanin kwai da lemon tsami

Allah ta’ala yabamu lpy da abinda lapiyar xataci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *