
Hukumar da ke yaƙi da fataucin mutane a Najeriya, NAPTIP ta ce ta ceto wata yarinya ƴar shekara biyu da aka yi safararta zuwa jihar Abia daga Abuja.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Juma’a, ta ce hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ne suka kama wanda ya yi safararta, inda ake zargin ya sayar da da ita kan naira 100,000.
“Mun samu nasarar ceto Chiamaka Favor, bayan safararta daga Abuja zuwa Aba a watan Febrairun 2025.
“Ana zargin wanda ya yi safararta ya yi aiki da wasu ƙungiyoyin safarar mutane uku a Abuja – sannan ya sayar da ita ga wani kan naira 100,000. Muna ci gaba da bincike,” in ji NAPTIP.
Hukumar ta kuma yi kira ga iyayen yarinyar ko ƴan uwanta da su hanzarta su tuntuɓe ta domin karɓar ƴarsu.