Thursday, January 22
Shadow

An fara Magudun zaben shekarar 2027>>Atiku Abubakar ya koka

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya koka da cewa, an fara magudin zaben shekarar 2027.

Ya bayyana hakan a shafinsa na sada zumunta inda yace an fara hakannne ta hanyar kaucewa gyaran dokar zabe.

Ya zargi majalisar tarayya da kaucewa gyara dokar zabe wadda zata sa kada a maimaita kuskuren da aka tafka a zaben shekarar 2023.

Atiku yace idan ba’a gyara dokar zaben ba ba lallai a samu sakamakon zabe sahihi a zaben shekarar 2027 ba.

Karanta Wannan  Shugaba Tinubu ya gana da Sarki Charles na Ingila

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *