
An gargadi su Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, da Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, da Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi su daina zuga ‘yan Najeriya kan mulkin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Wani dattijon jihar Legas, Chief Adesunbo Onitiri ne ya bayyana hakan a wata ganawa dashi.
Yace irin maganganun da wadannan ‘yan siyasar ke yi na iya kawo tarnaki wa tsarin siyasar kasarnan.
Yace su rika saka kishin kasa da al’ummarsu a cikin kalamansu.
Yace musamman Atiku dake neman ya binciko wasu laifukan shugaban kasar daga kasar Amurka dan hanashi takara a zaben shekarar 2027, yace hakan ba daida bane kuma ba zasu amince da hakan ba.