
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce jami’anta sun kama wani dattijo mai suna Ayuba Ashiru mai shekara 80 da kilo 2.3 na miyagun ƙwayoyi.
A wata sanarwa da kakakin hukumar na ƙasa Femi Babafemi ya fitar wadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 14 ga Mayun 2025 a yankin Dogarawa da ke ƙaramar hukumar Sabon Garin jihar Kaduna ne bayan samun bayanan sirri a game da harƙallarsa.
Sanarwar ta ce an taɓa kama Ashirun bisa fataucin miyagun ƙwayoyi, aka ɗaure na shekara goma tsakanin 2014 zuwa 2024.
“Ya ce ya kasance a harƙallar fataucin miyagun ƙwayoyi na tsawon shekara 46,” kamar yadda sanarwar ta nuna.
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa jami’an hukumar sun kama wata dattijuwa mai suna Uloma Uchechi Sunday mai shekara 82 da ƴarta mai shekara 32 mai suna Chisom Uchechi a jihar Abia da miyagun ƙwayoyi.