Saturday, December 20
Shadow

An kama Sanata Elisha Abbo saboda zargin Aikata Alfasha da wata me kananan shekaru

Hukumomin ‘yansanda sun kama sanata Elisha Abbo Saboda zargin aikatawa wata yarinya Fyade.

Rahoton yace Tsohon sanatan wanda ya wakilci Adamawa ta Arewa ya mika kansa wajan ‘yansanda a Abuja bayan da aka zargeshi da yiwa yarinya me shekaru 13 fyade.

Iyayen yarinyar sun yi zargin cewa, sanata Senator Aishatu Dahiru Ahmed (Binani) ta je har gidansu inda ta rokesu da kada su fitar da maganar.

Hakanan shima sanata Elisha Abbo ya rika aikawamahaifin yarinyar kudade da shirin kulle musu baki.

Dan Rajin kare hakkin bil’adama kuma Lauya, Deji Adesogan ne ya bayyana hakan sannan yace har yanzu sanata Elisha Abbo na daure a hannun ‘yansanda.

Karanta Wannan  Najeriya na son siyo irin wadannan jiragen 12 daga kasar Amurka dan magance matsalar tsaro

Wannan dai ba shine karin farko da Sanata Elisha Abbo ya shiga karma-karma ba, a baya ya taba cin zarafin wata mata a ofishin sayar da kayan biyan bukatar jima’i a Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *