Thursday, June 5
Shadow

An kama tsaffin shuwagabannin kamfanin man Fetur na kasa da aka sauke satin da ya gabata bisa zargin sun sace kudaden da aka ware dan gyaran matatun man Najeriya, An gano Naira Biliyan 80 a Asusun daya daga cikinsu

Rahotanni sun bayyana cewa, an kama tsaffin shuwagabannin matatun man fetur da aka sauke satin daya gabata saboda zargin sace kudaden da aka ware dan gyaran mamatun man fetur din.

Matatun man fetur din sune Warri, Fatakwal da Kaduna.

Jimullar kudaden da ake zarginsu da sacewa sun kai Dala $2,956,872,622.36.

A matatar man fetur ta Fatakwal ana neman dala $1,559,239,084.36 a yayin da a matatar man fetur ta Kaduna ana neman dala $740,669,600 inda a matatar man Warri ana neman dala $656,963,938.

Hakanan wata Majiya tace an samu Naira Biliyan 80 a asusun daya daga cikin manyan ma’aikatan.

Ana dai zargin wadannan shuwagabannin da yaudarar ‘yan Najeriya musamman game da gyaran matatar man Warri.

Karanta Wannan  Nifa ba da son raina na dawo Najeriya ba, garkuwa dani aka yi>>Inji Nnamdi Kanu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *