Tuesday, June 18
Shadow

An kashe sojojin Isra’ila huɗu a Rafah

Rundunar sojin Isra’ila ta ce an kashe sojojinta hudu a Rafah da ke kudancin Gaza.

A cewar wata sanarwa, sun mutu ne a lokacin da wani gini da aka maƙare da bama-bamai ya ruguje.

Biyu daga cikin sojojin ƴan shekara 19 ne, wanda ya girme musu kuma yana da shekara 24.

Sanarwar ta ƙara da cewa ƙarin wasu sojoji da dama kuma sun samu munanan raunuka.

Kimanin sojojin Isra’ila 300 ne suka mutu tun bayan kaddamar da mamaya a Gaza.

Yayin da yaƙin ya yi sanadin rasuwar Falasɗinawa 37,000, a cewar ma’aikatar lafiya ta Hamas.

Karanta Wannan  Masu zanga-zanga sun yi artabu da ƴan sandan Isra'ila

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *