Babban fasto, Primate Ayodele ya bayyana abubuwan da zasu faru a shekarar 2025 kamar yanda ya saba yi duk shekara inda yake ikirarin an masa wahayi.
Faston yace wasu daga cikin abubuwan da aka masa wahayi shine cewa za’a saki shugaban kungiyar IPOB dake son kafa kasar Biafra watau, Nnamdi Kanu, sannan matsin rayuwa zai karu a shekarar ta 2025.
Yace ya kuma gano cewa wani gwamna zai mutu, sannan za’a yi yunkurin kashe wani shugaban kasa ta hanyar zuba masa guba amma zai tsallake, saidai be bayyana kowane shugaban kasa bane.
Ya kuma za’a samu matsalar kisan jami’an tsaro na FBI da CIA na kasar Amurka.