Gwamnatin jihar Kano, a karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf ta sanar da goyon bayan masu zanga-zangar kan tsadar rayuwa.
Gwamnan da kansa ne ya bayyana hakan a wajan wani taro na masu ruwa da tsaki da aka gudanar ranar Laraba a Kano.
Gwamnan yace muddin za’a yi zàngà-zàngàr cikin tsari ba tashin hankali zai karbi masu zanga-zangar a fadar gwamnati.
Yace idam suna so ma zai shiga shima a yi dashi.
Gwamnan yace kundin tsarin Mulkin Najeriya ya bayar da damar yin zanga-zangar.
Saidai wannan ra’ayi nasa ya sha banban dana tsohon gwamnan jihar wanda ake ganin me gidansa ne watau Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.
A baya dai mun samu rahoton cewa, Kwankwaso ya bayar da shawarar a hakura da yin zanga-zangar a bari sai idan lokacin zabe yayi a fito a zabi wanda ake so.
A wani rahoton me kama da wannan kuma mun samu cewa, Wani rahoton sirri daya bayyana yace Kwankwaso na daya daga cikin manyan mutanen da aka baiwa kwangilar hana zanga-zangar musamman a jihar Kano, ganin cewa yana daya daga cikin masu fada aji na jihar.