Hukumar ‘yansanda a Birnin Jos na jihar Filato ta tabbatar da fargabar dasa bam a birnin.
Saidai ta musanta wannan jita-jita.
Kakakin ‘yansandan jihar, DSP Alfred Alabo ya tabbatarwa manema labarai cewa maganar dasa bam din ba gaskiya bane.
Yace ranar Talata ne aka fara yada jitajitar kuma jami’an su da suka kware wajan kula da bam sun isa wajan inda suka tabbatar da babu bam a inda ake rade-radin.