Rahotanni sun bayyana cewa,akwai rade-radin wasu manyan jami’n gwamnatin Shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu zasu yi murabua.
Daga cikin wadanda ake rade-radin akansu akwai shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar, Femi Gbajabiamila.
A jiya ne dai kakakin shugaban kasar, Ajuri Ngelale yayi murabus wanda hakan ya jawo cece-kuce sosai akan siyasar fadar shugaban kasar.