Thursday, June 5
Shadow

Ana rade-radin an fara zartar da shari’ar Musulunci a jihohin Yarbawa inda har aka yankewa wannan mutumin hannu saboda sata, mutumin yayi karin bayani

A cikin kwanakinnan Hotunan wani mutum da guntulallen hannu ya bayyana a kafafen sadarwa inda ake ikirarin cewa an yanke masa hannu ne bisa laifin sata a jihar Kwara inda aka fara zartas da shari’ar Musulunci.

Saidai a hirar mutumin me suna Lanlege Samuel Adewale da kafar yada labarai ta Leadership yace ‘yan Bindiga masu garkuwa da mutanene suka masa wannan aika-aika.

Yace daya daga cikin masu garkuwa da mutanenne ya kai masa sara a wuya shine ya kai hannunsa ya tare shin hannunsa na hagu ya fita.

Ya bayyana hakanne bayaj da ‘yansanda suka kubutar dashi da dan uwansa daga hannun masu garkuwa da mutanen.

Karanta Wannan  Ji Yanda Tsohon Ministan Sufuri Amaechi ya bayar da labarin yanda Allah ya tuka motarsa bayan da bacci ya kwasheshi yana tsaka da tuki daga Kaduna zuwa Abuja

Da yake bayar da labarin yanda aka yi garkuwa dashi, yace ranar Lahadi suna tafiya akan mashin a Ogbe dake karamar hukumar Yagba West ta jihar Kogi sai ‘yan Bindigar su 8 suka fito daga daji suka kamasu.

Yace a kokarin tserewa daga hannun masu garkuwa da mutanen ne a inda suke tsare dasu a Babanla dake karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara daya daga cikin masu garkuwa da mutanen ya yanke masa hannun hagu.

Yace sun barshi a kwance ya mutu sai bayan da jami’an tsaro suka ganshi ne suka kai masa dauki sannan aka kaishi Asibiti.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *