Monday, December 16
Shadow

Atiku ya jajanta wa Tinubu dangane da “zamewar” da ya yi

Mutumin da shugaba Tinubun ya kayar a zaɓen 2023, Atiku Abubakar na jam’iyyar adawa ta PDP, ya ce yana jajanta wa Bola Tinubu dangane da “zamewar” da ya yi.

“Ina matukar jajanta wa shugaba Bola Tinubu dangane da ɗan hatsarin da ya samu a lokaci da yake ƙoƙarin zagaya masu fareti ranar dimokaraɗiyya. Ina fatan lafiyar lau.”

A baya-bayan nan dai an ga yadda tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar ke ƙara ƙaimi wajen yin hamayya ta fuskar sukan abubuwan da yake ganin gwamnatin ba ta yi daidai ba.

Karanta Wannan  Bama tunanin hadewa da kowace jam'iyya>>PDP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *