Sunday, December 21
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Lura da irin Arzikin da Allah yawa Najeriya, bai kamata akwai talaka a kasarnan ba>>Inji Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Lura da irin Arzikin da Allah yawa Najeriya, bai kamata akwai talaka a kasarnan ba>>Inji Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Lura da irin Arzikin ma'adanan karkashin kasa da Allah yawa kasarnan, bai kamata ace akwai talaka a kasarba Shugabab ya bayyana hakane a wajan taro kan Arzikin ma'danan karkashin kasa da Allah yawa Najeriya da ya gudana a Abuja. Sakataren Gwamnatin tarayya, George Akume ne ya wakilci shugaban kasar a wajan taron. Ya bayyana cewa, Gwamnatin tarayya zata yi dukkan mai yiyuwa wajan samar da yanayi me kyau na zuba hannun jari a kasarnan ta bangaren ma'adanan karkashin kasa. Sannan ya yi kira ga kasashen Afrika dasu yi amfani da ma'adannan karkashin kasar da Allah ya hore musu dan karfafa tattalin arzikin su.

Kwana hudu da suka gabata na musulunta, amma ana gayamin za’a koreni daga wajan aiki na idan ban bar Musulunci ba, Saidai na zabi Allah da Addinin Musulunci maimakon aikin nawa>>Inji Ba’amurke, Martin

Duk Labarai
Wani ba'amurke me suna Martin ya bayyana cewa, kwanaki 4 da suka gabata ya shiga addinin Musulunci. Yace amma kuma an matsa masa a wajan aikinshi cewa sai ya bar addinin Musulunci. Yace shi kuma ya zabi ya ci gaba da kasancewa a addinin Musulunci. ya wallafa hakane a shafinsa na sada zumunta. https://twitter.com/D_Maaartin/status/1978489878590406762?s=19
Farashin Man fetur ya kai Naira dubu(1000) kan kowace lita a yayin da Layuka suka fara tsawo a gidajen man fetur

Farashin Man fetur ya kai Naira dubu(1000) kan kowace lita a yayin da Layuka suka fara tsawo a gidajen man fetur

Duk Labarai
Rahotanni sun ce Laiyukan ababen hawa sun fara yawa a gidajen Man fetur a sassa daban-daban na Najeriya a yayin da ake fama da hauhawar farashin man a garuruwa daban-daban. Rahoton yace Farashin litar man fetur din ya kai Naira 1000. 'Yan kasuwar man fetur sun zargi Depot dake sayar musu man a farashin sari da cewa, sune suka sa man yayi tsada dan sun kara farashin da suke sayar musu da man. Hakan na zuwane duk da ga matatar man fetur ta Dangote a Najeriya kuma ya fara kai man fetur din zuwa wasu gidajen man kyauta ba kudin dako.
Lauyoyin Nnamdi Kanu sun bayyana cewa, basu yadda da Sakamakon gwajin Lafiyar da aka masa ba inda suka ce ko jininsa ba’a dauka ba ta yaya za’a ce yana da lafiyar da zai iya ci gaba da tsayawa a gaban kotu?

Lauyoyin Nnamdi Kanu sun bayyana cewa, basu yadda da Sakamakon gwajin Lafiyar da aka masa ba inda suka ce ko jininsa ba’a dauka ba ta yaya za’a ce yana da lafiyar da zai iya ci gaba da tsayawa a gaban kotu?

Duk Labarai
Lauyoyin Nnamdi Kanu sun bayyana cewa, basu yadda da sakamakon gwajin Lafiyar da aka masa ba inda suka ce ta yaya gashi an tabbatar bashi da lafiya amma ace wai zai iya tsayawa a gaban Kotu. Lauyoyin bayan zaman kotun a yau, Alhamis sun bayyana cewa, suna kira ga kungiyar Likitoci ta kasa data kiyaye kada ta batawa kanta suna. https://twitter.com/General_Somto/status/1978774791155806233?t=L8YzAemwn84Rd-Nqt73sww&s=19 A baya dai sakamakon da likitoci suka fitar akan Lafiyar Nnamdi Kanu sun ce zai iya ci gaba da tsayawa a gaban kotu dan ci gaba da masa shari'a sannan kuma Asibitin sha ka tafi na DSS zai iya ci gaba da dubashi saboda rashin lafiyar tasa bata yi tsanani ba.
Kalli Bidiyon: Wallahi ‘yan Darika 6 ne suka kirani suka ce sun Tuba sun daina Darika bayan da Malam Lawal Triumph ya kare kansa a gaban Kwamitin Shura>>Inji Malam

Kalli Bidiyon: Wallahi ‘yan Darika 6 ne suka kirani suka ce sun Tuba sun daina Darika bayan da Malam Lawal Triumph ya kare kansa a gaban Kwamitin Shura>>Inji Malam

Duk Labarai
Malam ya bayyana cewa, Bayan da Malam Lawal Triumph ya kare kansa a gaban Kwamitin Shura na Kano, akwai 'yan darika Guda 6 da suka kirashi suka ce sun daina Darika. Yace cikinsu hadda mace. Malam Yayi kira ga Gwamnan Kano da ya daina yadda ana sakashi a wannan rikicin inda yace ya barsu da 'yan Darikar su sun san yadda zasu yi dasu. https://www.tiktok.com/@ali_d_abba/video/7561178610330045718?_t=ZS-90b3UnM1PUn&_r=1
Wata Sabuwa, Kalli Bidiyon: Ana zargin Kudi aka baiwa matashinnan na Maiduguri ya yi Ridda ya koma Kirista

Wata Sabuwa, Kalli Bidiyon: Ana zargin Kudi aka baiwa matashinnan na Maiduguri ya yi Ridda ya koma Kirista

Duk Labarai
Matashinnan na Maiduguri da yayi ridda ya koma Kirista ya jawo cece-kuce sosai a kafafen sada zumunta. Wasu sun rika tambayar ko yana cikin hayyacinsa ya dauki wannan mataki? Saidai a nasa sharhin, Abdullahi yayi zargin cewa, Kudi aka baiwa matashin ya bar Addinin Musulunci. Saurari Sharhin Abdullahi a Bidiyon kasa https://www.tiktok.com/@abdallahtoyota0/video/7561065754917899528?_t=ZS-90b1uA5bpzM&_r=1
Ba sai an je da yawa ba, Shekaru 4 sun isheni in gyara Najeriya idan aka zabeni shugaban kasa>>Inji Peter Obi

Ba sai an je da yawa ba, Shekaru 4 sun isheni in gyara Najeriya idan aka zabeni shugaban kasa>>Inji Peter Obi

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour Party a zaben shekarar 2023, Peter Obi ya bayyana cewa, shekaru 4 sun isheshi ya gyara Najeriya idan aka zabeshi shugaban kasa. Peter Obi ya kuma baiwa magoya bayansa tabbacin zai tsaya takarar shugaban kasa a 2027. Ya bayyana hakane a ganawar da yayi da manema labarai a Abuja ranar Laraba. Ya kuma ce yana da Kwarewa da cancantar zama shugaban kasa a Najeriya. Obi ya kuma bayar da tabbacin cewa, duka 'yan Najeriya dake son Najeriya da arziki zasu taru ne dan kayar da Gwamnati me ci.
Farashin kayan abinci ya sauka sosai wadda rabon a ga haka tun shekaru 3 kenan

Farashin kayan abinci ya sauka sosai wadda rabon a ga haka tun shekaru 3 kenan

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, alkaluman farashin kayan abinci ya sauka a Najeriya inda a yanzu yake a maki 18.02 a watan Satumba daya gabata. Idan aka kwatanta da watan Augusta daya gabata, Alkaluman na matsayin maki 20.12 wanda hakan ke tabbatar da an samu sauki sosai. Hukumar kula da kididdiga ta kasa, NBS ce ta bayyana hakan a sanarwar data fitar ranar Laraba. Rabon da makin na NBS ya sakko kasa da 20, shekaru 3 kenan.
Nnamdi Kanu na da lafiyar da zai iya fuskantar shari’a – Likitoci

Nnamdi Kanu na da lafiyar da zai iya fuskantar shari’a – Likitoci

Duk Labarai
Tawagar ƙwararrun likitoci a Najeriya, ƙarƙashin jagoranci shugaban ƙungiyar Likitocin ƙasar, sun tabbatar da cewa rashin lafiyar da aka ce na damun Nnamdi Kanu ba wata babbar damuwa ba ce. Maishari'a, James Omotosho ne ya umarci tawagar likitocin ta duba lafiyar Kanu, bayan da lauyoyinsa suka yi iƙirarin cewa yana fama da wata jinya. Cikin rahoton binciken tawagar ƙwararrun likitocin, da aka miƙa wa kotu ranar 13 ga watan Oktoban da muke ciki, ya ce rashin lafiyar da ke damun Kanu ba mai barazana ba ce. Tawagar likitocin ta ce bayan auna lafiyar Kanu sun tabbatar da cewa za a iya ci gaba da yi masa shari'a, domin kuwa zai iya halartar kotu. Bayan karɓar rahoton, Maishari'a Omotosho ya ce kotun ta gamsu da rahoton don haka za a ci gaba da shari'ar.