Sunday, December 21
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyon: An yaye jami’an tsaro na musamman guda 380 da za su yi yaki da masu kwacen waya a Kano

Kalli Bidiyon: An yaye jami’an tsaro na musamman guda 380 da za su yi yaki da masu kwacen waya a Kano

Duk Labarai
An kammala horaswa da kuma yaye jami'an hukumar KOSSAP da aka samar na musamman a jihar Kano da zasu rika yaki da kwacen waya. Jami'an su 380 an kammala yaye su ne a ranar Lahadi inda kuma zasu fara aiki nan ba da jimawa ba. An shafe sati biyu ana basu horo. Matsalar kwacen waya yayi kamari a jihar Kano inda ake kashe mutane ana kwace musu wayoyi.
Lauya ya garzaya kotu inda yake neman ta hana Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan tsayawa takarar shugaban kasa a 2027

Lauya ya garzaya kotu inda yake neman ta hana Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan tsayawa takarar shugaban kasa a 2027

Duk Labarai
Wani lauya me suna Johnmary JideObi ya shigar da karar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan kan neman kotu ta hanashi tsayawa takarar shugaban kasa a 2027. Ya shigar da karar ne ranar Litinin a babbar kotun tarayya dake Abuja. Yace idan Goodluck Jonathan ya sake cin zabe zai yi shekaru fiye da 8 da doka ta yadda kowane shugaba yayi. Dan hakane yake neman a hanashi tsayawa takarar shugaban kasa a 2027.
Najeriya na sa ran haƙo gangan ɗanyen mai miliyan1.8 a kullum

Najeriya na sa ran haƙo gangan ɗanyen mai miliyan1.8 a kullum

Duk Labarai
Shugaban kamfanin mai na Najeriya, NNPCL, Bayo Ojulari, ya bayyana kyakkyawan fatan cewa ƙasar zata dinga haƙo gangan ɗanyen mai miliyan1.8 kafin ƙarshen shekarar 2025. Kafar watsa labarai ta Channels TV ta ce shugaban kamfanin ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, yayin da ya ke sanar da shugaba Bola Tinubu kan ayyukan kamfanin a jihar Legas. Mista Ojulari ya ce gyare-gyaren da suka yi a watannin Agusta da Satumba zasu taimaka wurin samar da ci gaba a wannan watan. Inda ya ƙara da cewa “Muna fatan kafin ƙarshen shekarar nan mu kai ga haƙo aƙalla gangan ɗanyen mai miliyan ɗaya da dubu 800 a kullum. ” A halin yanzu dai ƙasar na haƙo ganga miliyan 1.71 a kullum. Kuma ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen da ke gaba-gaba wurin samar da ɗanyen mai a ƙungiyar OPEC a duniya....
Bincike ya samu Ministan kimiyya na Najeriya da ‘mallakar takardun boge’

Bincike ya samu Ministan kimiyya na Najeriya da ‘mallakar takardun boge’

Duk Labarai
Wani bincike da jaridar Premium Times ta yi ya nuna cewa ana zargin ministan kimiyya da fasaha na Najeriya, Uche Nnaji, da yin takardun kammala karatu na boge, lamarin da ke ci-gaba da janyo cece-kuce a ƙasar. Binciken da jaridar ta Premium times ta wallafa ya ce an gano cewa ministan ya miƙa takardun bogin ga majalisar dattawan ƙasar domin tattance shi, bayan shugaban Bola Ahmed Tinubu ya miƙa sunansa cikin waɗanda yake so ya bai wa muƙamin minista a shekarar 2023. Jaridar ta yi ikirarin cewa takardun shaidar kammala karatun digiri da na bautar ƙasa na Mr Nnaji duka na boge ne. Inda ta ƙara da cewa masu suka sun ce ministan bai kammala karatun digirin ba, haka kuma takardar shaidar bautar ƙasar da ya miƙa wa ofishin sakataran gwamnatin tarayya da hukumar tatta...
Tinubu ya buƙaci NAHCON ta rage kuɗin Hajjin bana

Tinubu ya buƙaci NAHCON ta rage kuɗin Hajjin bana

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci hukumar jin daɗin alhazai ta Najeriya NAHCON da ta rage kuɗin Hajjin bana, inda ya buƙaci hukumar ta fito da sabon kuɗin nan da kwana biyu. Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ne ya bayyana wannan buƙatar a ganawarsa da shugabannin hukumar a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja a ranar Litinin. Ya yi kira da a samu ƙarin haɗin kai tsakanin hukumar a matakin ƙasa da takwarorintna na jihohi ciki har da gwamnoni domin a samu sauƙin gudanar da aikin Hajjin na bana. Da yake ganawa da manema labarai bayan taron, mataimakin shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Sanata Ibrahim Hadejia ya ce an yi taron ne domin ƙarƙare shirye-shiryen Hajjin na bana, ciki har da tattaunawa game da kuɗin kujera. "Saboda yadda farashin naira ya haɓaka da k...
Kalli Bidiyo: Dole a Hakura a Fadi gaskiya, ‘Yan Darikar Sufaye su suka fi son Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam)>>Inji Digital Imam

Kalli Bidiyo: Dole a Hakura a Fadi gaskiya, ‘Yan Darikar Sufaye su suka fi son Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam)>>Inji Digital Imam

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Sheikh Nura Khalid wanda aka fi sani da Digital Imam ya bayyana cewa, 'yan Darikar Sufaye su suka fi son Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam). Malam yace abin ba zai yiwa wasu dadin ji ba amma dole a fadi gaskiya. Ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda yace asalin Sufaye sun samo asaline daga Zuhudu, watau Gudun Duniya. https://www.tiktok.com/@shaaweuei5p/video/7557941385383496967?_t=ZS-90JnomaD6XY&_r=1
Kalli Bidiyo: Bayan da Ya Musuluntar da Baturiyar da suke waka tare, Mawaki 442 ya kuma koya mata Sallah

Kalli Bidiyo: Bayan da Ya Musuluntar da Baturiyar da suke waka tare, Mawaki 442 ya kuma koya mata Sallah

Duk Labarai
Tauraron mawakin Batsa, wanda yace ya tuba daga wakokin batsa da yake yi a baya, 442 ya musuluntar da baturiyar da suke waka tare. A baya, Hutudole ya kawo muku yanda 442 ya nakaltawa Baturiyar kalmar Shahada inda ta karbi Musulunci. A yanzu kuma, 442 ya koya mata yanda ake Sallah An ga 442 yana limanci yayin da baturiyar ke binsa a baya. https://www.tiktok.com/@mr442_/video/7557848257540476167?_t=ZS-90Jlt9cmLFB&_r=1
Duk da Dangote na kai musu man da suka saya da tankokin Motocinsa Kyauta, Har yanzu gidajen man fetur basu rage farashin ma nasu ba

Duk da Dangote na kai musu man da suka saya da tankokin Motocinsa Kyauta, Har yanzu gidajen man fetur basu rage farashin ma nasu ba

Duk Labarai
Rahotanni sun ce duk da Dangote na daukar man fetur din da gidajen mai suka siya da tankokin motocin sa yana kai musu kyauta. Har yanzu gidajen man basu rage farashin man fetur din da suke sayarwa ba. An yi tsammanin tunda babu kudin dakon mai da gidajen man fetur din ke biya, Dangote na kai musu kyauta da tankokinsa, farashin man da suke sayarwa zai sakko kasa. Saidai hakan bata faru ba inda hadda gidan man MRS wanda shine yafi kusa da Dangote wanda suka yi hadaka, shima a wasu wajajen farashin litarsa na kaiwa har Naija 875, kamar yanda jaridar Punchng ta ruwaito bayan yin zagaye ta ga yanda ake sayar da mai a gidajen man.
Kalli Bidiyo: Likafa ta yi gaba inda aka ga Iftihal Madaki a karo na biyu tana rawa da Soja Boy

Kalli Bidiyo: Likafa ta yi gaba inda aka ga Iftihal Madaki a karo na biyu tana rawa da Soja Boy

Duk Labarai
An sake ganin Tauraruwar Tiktok, wadda a baya ke yin Bidiyo da Hijabi amma aka ganta da su Soja Boy suna rawa wadda bata dace ba ta sake yin sabon Bidiyo da Soja Boy din. A wannan karin ma an ga Iftihal Madaki na rawa tare da Soja Boy ba Hijabi. Lamarin ya kara tabbatarwa da mutane cewa lallai itace domin kuwa ta wallafa Bidiyo a shafinta na Tiktok suna wakar tare da Soja Boy. https://www.tiktok.com/@bigdoxxx/video/7557856750192446721?_t=ZS-90JecHofmGu&_r=1 https://www.tiktok.com/@iftih_al/video/7557864109241339157?_t=ZS-90JfgT1BQET&_r=1