PENGASSAN ta amince ta janye yajin aiki bayan Dangote ya amince ya mayar da ma’aikata 800 da ya kora bakin aiki
Ƙungiyar manyan ma'aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya, PENGASSAN ta amince da jingine yajin aikin da shiga bayan samun saɓani da matatar mai ta Dangote
Yajin aikin na zuwa ne bayan PENGASSAN ta zargi mattaar da korar fiye da ma'aikata 800 saboda sun nuna sha'awar shiga ƙungiyar.
Gwamnatin Najeriya ce ta shiga tsakani a sasancin ɓangarorin biyu da ake yi tun ranar Litinin, to amma sai a yau Laraba ne aka cimma matsaya.
Cikin wata sanarwa da ma'aikatar kwadagon ƙasar ta fitar ta ce matatar ta amince da mayar da ma'aikatan da ta kora domin su ci gaba da aiki da ita.
"Babu ma'aikacin da zai cutu sakamakon saɓanin matatar Dangote da PENGASSAN," a cewar sanarwar.
A nata ɓangare, ƙungiyar ta PENGASSAN ta ''amince ta fara shirye-shiryen janye yajin aikin''.
Tun bayan fara...








