Friday, December 19
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Duk da rage farashin man fetur da Dangote yayi, gidajen mai har yanzu suna sayarwa a tsohon farashi me tsada

Duk da rage farashin man fetur da Dangote yayi, gidajen mai har yanzu suna sayarwa a tsohon farashi me tsada

Duk Labarai
Rahotanni sun ce har yanzu gidajen man fetur na sayar da man a farashi me tsada duk da rage farashin da matatar man fetur ta Dangote ta yi. A makon daya gabata ne Matatar man ta sanar da rage farashin daga Naita 865 zuwa naira 820 akan kowace lita musamman tace saboda tankokin man ta 1000 zasu fara jigilar man zuwa gidajen mai kyauta. Saidai binciken da jaridar Punchng ta yi yace har yanzu a jihohin Legas da Ogun da sauran wasu jihohi gidajen man basu fara sayar da man a sabon farashi ba.
Wata Sabuwa: Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari na daga cikin wadanda suka aikawa matar shugaban kasa, Remi Tinubu da tallafi na murnar zagayowar ranar Haihuwarta, wanda a yanzu kudin sun haura Naira Biliyan 20

Rahotanni sun bayyana cewa, Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari na daga cikin wadanda suka aikawa matar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, Watau Remi Tinubu da tallafin data nema na zagayowar ranar Haihuwarta. Remi Tinubu ta nemi a tara mata kudi a yayin data cika shekaru 65 da haihuwa inda tace za'a yi amfani da kudin wajan kammala ginin hedikwatar dakin karatu na kasa. Tuni aka sanar cewa kudin sun kai sama da Naira Biliyan 20 wadanda 'yan Najeriya suka tara mata. Saidai wani abin mamaki shine, cikin jerin mutanen da suka tura mata da kudaden tallafin hadda tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari. Hakan na zuwane duk da cewa, tun kamin Uwargidan shugaban kasar ta fara neman wannan tallafin Buhari ya rasu. Abin ya zowa mutane da yawa da mamaki matuka. ...
Bariki ba dadi, Gidan iyaye yafi dadi, Dan Allah ku daina zagin mu, ku rika mana Addu’a mu da muka fito daga gidan iyayen mu muka shiga bariki, Allah ya shiryemu>>Inji A’isha Beauty

Bariki ba dadi, Gidan iyaye yafi dadi, Dan Allah ku daina zagin mu, ku rika mana Addu’a mu da muka fito daga gidan iyayen mu muka shiga bariki, Allah ya shiryemu>>Inji A’isha Beauty

Duk Labarai
A'isha Beauty ta bayyana cewa, Gidan iyaye yafi dadi. Ta bayyana hakane a shafinta na sada zumunta inda tace masu zaginsu, su da suka baro gidan iyayensu suka shiga bariki su daina. Ta yi rokon a rika musu addu'ar Allah ya shiryesu. Ta kuma yiwa masu shirin barin gidan iyayensu su shiga bariki addu'ar Allah ya karkatar da zuciyarsu zuwa daidai. https://www.tiktok.com/@aysha.beauty50/video/7553099428987555080?_t=ZS-901OilwIYxF&_r=1
Kalli Bidiyo: Wannan me hakar kabarin ya bayyana irin ni’imar da ya taba gani a cikin wani kabari da ta bashi mamaki

Kalli Bidiyo: Wannan me hakar kabarin ya bayyana irin ni’imar da ya taba gani a cikin wani kabari da ta bashi mamaki

Duk Labarai
Wannan wani me hakar Kabari ne da ya bayar da labarin irin ni'imar da ya taba gani a cikin wani kabari. Yace yana hakar sabon kabari ne shine kafarsa ya zurma cikin wani kabari, yace kawai sai yaji wata irin ni'ima har cinyarsa. https://www.tiktok.com/@g_fresh_alameen0/video/7553053843660082444?_t=ZS-901B0WxBJj7&_r=1 Ya kuma bayar da labarin wasu kaburburan da yace sai kasusuwa ake gani.
An sace danyen man fetur na zunzurutun kudi har Naira Tiriliyan N8.41tn

An sace danyen man fetur na zunzurutun kudi har Naira Tiriliyan N8.41tn

Duk Labarai
Rahotanni daga hukumar kula da harkar man fetur a Najeriya, watau Nigerian Upstream Petroleum Regulatory Commission, sun ce an sace jimullar danyen man fetur na Naira Tiriliyan N8.41tn. Rahoton yace an yi wannan gagarumar satar ne a tsakanin shekarun 2021 da 2025. Saidai rahoton yace a yanzu an samu raguwar satar danyen man ba irin a baya ba amma duk da haka jimullar yawan danyen man da aka sace ya nuna gazawar gwammati. Me sharhi akan Almuran yau da kullun, Professor Ayoade yace abin takaici ne ace an tafka irin wannan asarar amma babu wanda aka hukunta.
Da Duminsa: Bayan da yace bai yadda a bincikeshi ba kan Gwamnan rikon kwarya na watanni 6 da yayi a jihar Rivers ba, Ibas ya gana da shugaba Tinubu, da shugaban EFCC da Ministan Kudi a daren jiya

Gwamnan rikon Kwarya na jihar Rivers, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas wanda ya shafe watanni 6 a mukamin ya gana da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a fadarsa dake Abuja da yammacin jiya, Laraba. Rahotanni daga Punchng sun ce ganawar ta samu halartar Ministan kudi, Wale Edun da kuma shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyode. Saidai ba'a samu bayani kan abinda suka tattauna ba. Hakan na zuwanw kwanaki 3 bayan da Ibas yace bai yadda da shirin binciken da majalisar jihar Rivers ke shirin yi masa ba inda yace Bincikensa kamar binciken shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne da majalisar tarayya domin shi Tinubu ne ya bashi aiki. Rahotanni sun ce Jihar Rivers me arzikin mai ta samu makudan kudaden shiga da suka Haura daruruwan Biliyoyin Naira a watanni 6 da Ibas yayi na gwamnan rikon kwarya.