Friday, December 19
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Matashi daga Kano, Ibrahim Bala ya kirkiro na’urar da zata taimaka wajan hana direbobi Hadari

Matashi daga Kano, Ibrahim Bala ya kirkiro na’urar da zata taimaka wajan hana direbobi Hadari

Duk Labarai
Wani matashi daga Kano me suna Ibrahim Bala ya kirkiro na'urar da zata hana direba bacci wanda hakan ake tsammanin zai rage yawan aukuwar Hadurra. Matashin yace ya kirkiro wannan na'ura ne bayan aukuwar hadarin motar da yayi sanadiyyar salwantar rayukan 'yan kwallon Kano wanda aka alakanta da baccin da ya dauke direbansu. Tuni dai tsohon hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya shiga gaba dan ganin wannan matashi ya samu tallafi.
Da Matatar Man fetur dina bata yi nasara ba da na talauce dan da duk kadarorina bankuna zasu kwace>>Inji Dangote

Da Matatar Man fetur dina bata yi nasara ba da na talauce dan da duk kadarorina bankuna zasu kwace>>Inji Dangote

Duk Labarai
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa, da Matatar mansa bata yi nasara ba da duka kadarorinsa za'a kwace ya koma kauye da zama. Yace dalili kuwa shine kadarorinsa ne ya bayar bankuna suka bashi bashin da ya gina matatar man fetur din tasa. Dangote yace an rika kiransa ana gargadin sa cewa Gwamnati ce kadai take irin wannan aikin gina matatar man fetur din da yake yi. Yace amma duk da haka yayi kunnen uwar shegu ya ci gaba.
Da Duminsa: NECO ta fitar da sakamakon jarabawar 2025 kuma an ci ba laifi

Da Duminsa: NECO ta fitar da sakamakon jarabawar 2025 kuma an ci ba laifi

Duk Labarai
Hukumar Shirya jarabawar kammala sakandare, NECO ta fitar da sakamakon jarabawar kuma kaso 60 cikin 100 na wadanda suka rubuta jarabawar sun yi nasara. An saki sakamakon jarabawar ne kwanaki 54 bayan rubutata. Ragistara na NECO, Farfesa Ibrahim Wushishi ya sanar da sakamakon jarabawar inda yace dalibai 1,358,339 ne suka rubuta jarabawar. Wanda suka ci jarabawar kuma sun kai 818,492 wanda hakan yake nufin kaso 60.26 cikin 100 sun ci jarabawar. Wadannan wadanda suka ci lissafi da turanci ne. Hakanan yace wadanda kuma suka ci 5 credit sun kai 1,144,496, wanda hakan ke nufin kaso 84.26.
Darajar Naira ta karu a kasuwar Canji

Darajar Naira ta karu a kasuwar Canji

Duk Labarai
Rahotanni daga babban bankin Najeriya, CBN yace darajar Naira ta karu inda aka sayi dalar Amurka akan Naira 1,497.5 Hakan ya fito ne daga babban bankin Najeriya, CBN inda kuma aka samu kudin ajiyar Najeriya a kasashen waje na dala ke kara hauhawa. Masana tattalin arziki sun ce hakan alamace ta cewa tattalin arzikin Najeriya na kara hauhawa. Wannan shine karo na farko da Naira ta je kasa da 1,500 akan kowace dala daya tun farkon shekarar 2025.
Buhari ne ya lalata Naira ya mata rugu-rugu, Inji tsohon kakakin majalisar Wakilai>>Yakubu Dogara

Buhari ne ya lalata Naira ya mata rugu-rugu, Inji tsohon kakakin majalisar Wakilai>>Yakubu Dogara

Duk Labarai
Tsohon kakakin majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya bayyana cewa, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne ya lalata Darajar Naira. Ya bayyana hakane a wajan wani taro da ya halarta inda yace Buga kudin Naira sama da Naira Tiriliyan 22.7 ne ya jawowa Kudin Naira karyewa. Yace an rika amfani da damar karbar dala wasu suna arzuta kansu fiye da kima a lokacin mulkin Buharin.
Allah bai yi Duniya dan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ba duk wanda yace Allah yayi Duniya dan Annabi karya yake>>Inji Malam Abdulrahman Umar

Allah bai yi Duniya dan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ba duk wanda yace Allah yayi Duniya dan Annabi karya yake>>Inji Malam Abdulrahman Umar

Duk Labarai
Malam Abdulrahman Umar Sautussunnah ya bayyana cewa, Allah bai yi Duniya dan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ba. Malam yace Allah ya yi Duniya dan a Bauta masaa ne. Yace duk wanda yace Allah yayi Duniya dan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) karya yake. https://www.tiktok.com/@abdurrahmanumarr/video/7550806244898950421?_t=ZS-8znQ4uagzbt&_r=1
Kalli Bidiyon: Wani mutum da ya taba taimakon wannan matar da Naira dubu dari biyar da hamsin yayi mamakin ganinta tana bara da ‘ya’yanta akan titi

Kalli Bidiyon: Wani mutum da ya taba taimakon wannan matar da Naira dubu dari biyar da hamsin yayi mamakin ganinta tana bara da ‘ya’yanta akan titi

Duk Labarai
Wani mutuk yace ya taba taimakon wannan matar da Naira 550,000 amma abin mamaki shine sai gata ya ganta tana bara da 'ya'yanta akan titi. Lamarin dai ya jawo cece-kuce sosai inda wasu ke cewa ko nawa mutum ke gareshi zasu iya karewa, wasu kuwa suna ganin akwai sakaci a lamarinta. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1967538943857189122?t=z1HGCNgOg_dZRzvWrWtAKA&s=19 https://www.youtube.com/watch?v=j0xF7esqXAY?si=AN7oY_9aWzkgHIjg
Soja Boy ya yi magana game da wannan hoton shi da Rahama Saidu a daki

Soja Boy ya yi magana game da wannan hoton shi da Rahama Saidu a daki

Duk Labarai
Tauraron mawakin Gambara me yawan amfani da kalaman batsa, wanda aka fi sani da Soja yayi martani bayan ganin wani hotonsa shi da Rahama Saidu a kan gado Hoton dai na AI wanda yayi ta yawo a kafafen sadarwa. Abin ya bashi dariya inda yace amma yanayin dakin ya burgeshi. Hakan na zuwane bayan da aka ga hotuna inda Soja Boy ya rungumi Rahama da kuma inda ya gaisa da ita.