Saturday, May 24
Shadow

Author: Auwal Abubakar

Kamfanin sadarwar Airtel ya sanar da tafka asarar Dala Miliyan $344 a kasuwancin sayar da data

Kamfanin sadarwar Airtel ya sanar da tafka asarar Dala Miliyan $344 a kasuwancin sayar da data

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Kamfanin sadarwa na Airtel ya sanar da tafka asarar Dala Miliyan $344 a wajan kasuwancin sayar da data. Kamfanin yace ta tafka asarar a watanni 9 da suka gabata wanda suka kare a karshen watan Disamba na shekarar 2024. A shekarar baya kamfanin ya samu kudin shiga daga kasuwancin sayar da data wanda suka kai dala miliyan $539. Hakan na faruwane yayin da yawan masu amfani da layin waya na Airtel suka karu wanda a yanzu sun kai Mutane Miliyan 56.6. Shugaban kamfanin, Dinesh Ba...
Jam’iyyar PDP ta lashe gaba dayan zaben kananan hukumomin da aka gudanar a jihar Osun

Jam’iyyar PDP ta lashe gaba dayan zaben kananan hukumomin da aka gudanar a jihar Osun

Duk Labarai
Rahotanni daga zaben kananan hukumomin jihar Osun da ya gabata ya nuna cewa, Jam'iyyar PDP ce ta lashe zaben a kafatanin kananan hukumomin jihar. Kwamishinan zabe na jihar, Hashim Abioye ne ya bayyana hakan bayan kammala zaben inda yace PDP ce ta yi nasara a kananan hukumomi 30 da mazabu 323 dake fadin jihar. Yace an samu nasarar kammala zaben cikin nasa. Yace Jam'iyyu 18 ne suka yi takara a zaben kuma PDP ce ta lashe zaben na kananan hukumomi dana kansiloli baki daya.
An kama magidanci da Abokinsa da sukawa Agolarsa fyàdè, suka dirka mata ciki

An kama magidanci da Abokinsa da sukawa Agolarsa fyàdè, suka dirka mata ciki

Duk Labarai
Mahukunta a jihar Legas sun kama magidanci dan kimanin shekaru 38 da abokinsa da suka hadu sukawa agolarsa me shekaru 14 fyade. Kakakin 'yansandan jihar, CSP Benjamin Hundeyin ya tabbatar da faruwar hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Asabar. Ya kara da cewa, mahaifiyar yarinyarce ta kai koke a ofishin 'yansanda dake yankin Okokomaiko na jihar. Rahoton yace sun dirkawa yarinyar ciki inda a yanzu tana dauke da cikin wata 9. Ya kara da cewa, da zarar an kammala bincike, za'a gurfanar da wanda ake zargin a kotu.
Ina alfahari da babana, ‘Yan hassada ne ke son bata masa suna>>Inji Dan Tsohon Shugaban kasa, Janar Sani Abacha

Ina alfahari da babana, ‘Yan hassada ne ke son bata masa suna>>Inji Dan Tsohon Shugaban kasa, Janar Sani Abacha

Duk Labarai
Dan tsohon shugaban kasa, Marigayi Janar Sani Abacha me suna Sadiq ya jinjinawa mahaifin nasa inda yace yana alfahari dashi. ya bayyana hakane a yayin da aka taso da guguwar sukar mahaifin nashi. Yace yawanci masu sukar mahaifin nashi suna yi ne saboda hassada da kuma wadanda suka ci amanarsa. Yace amma mahaifinsu shugaba ne na gari kuma yayi abinda ya kamata a kasarnan. Guguwar Sukar Janar Sani Abacha ta sake tasowane biyo bayan kaddamar da littafin da tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida yayi.
Gwamnatin tarayya ta yi gargadin a daina cin Ganda

Gwamnatin tarayya ta yi gargadin a daina cin Ganda

Duk Labarai
Ministan ci gaban Kiwo, Mukhtar Maiha ya gargadi 'yan Najeriya da su daina cin Ganda wadda ake yi da fatar dabbobi. Ministan yace akwai matsalar da cin gandar yakewa jikin dan adam. Ya kuma bayyana cewa, Gwamnatin tarayya na shirin samar da mayanka ta zamani wadda kowace sashe na jikin dabbar da aka yanka za'a iya fitar dashi cikin sauki ba tare da wahala ba. Ya kara da cewa, a jikin dabba babu abin yaddawa. Ya kara da cewa, a cikin kasafin kudin shekarar 2025 sun ware kudade masu yawa dan samar da gonaki da guraren kiwo na zamani
‘Yan Bindiga sun budewa motar matafiya wuta a hanyar Sokoto zuwa Minna, 2 sun Mùtù wasu sun jikkata

‘Yan Bindiga sun budewa motar matafiya wuta a hanyar Sokoto zuwa Minna, 2 sun Mùtù wasu sun jikkata

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan Bindiga sun budewa motar matafiya kirar Sharon akan hanyar Sokoto zuwa Minna wuta i da suka kashe mutane biyu a cikin motar wasu kuma suka jikkata. Lamarin ya farune a yayin da motar ta doshi mabiyar 'yan Bindigar. Rahoton daga kafar Zagazola Makama ya bayyana cewa, wanda aka kashe din mace da namiji ne. An garzaya da gawarwakin wadanda suka rasu da kuma wadanda suka jikkata zuwa Asibitin IBB Specialist Hospital dake Minna.
Hotuna:Kalli Yanda aka gano wasu matsafa dake kwakule Kaburbura suna sace sassan jikin mutane a jihar Borno

Hotuna:Kalli Yanda aka gano wasu matsafa dake kwakule Kaburbura suna sace sassan jikin mutane a jihar Borno

Duk Labarai
An gano yanda wasu da ake zargin matsafane ke kwakule kaburbura bayan a binne a jihar Borno inda suke sace sassan jikin gawargwakin Lamari na kwanannan da aka gano shine wanda ya faru a makabartar Ramon Yashi dake Bayan Kwatas a cikin Birnin Maiduguri. An ga sabon kabari da aka binne amma an kwakuleshi an dauke gawar dake ciki, mazauna unguwar sun fara fargabar cewa da wuya idan babu matsafa ne suka aikata hakan ba. Wani shaida ya bayyanawa majiyarmu cewa, sun hango gawa na yawo akan ruwa, kuma sun je bakabarta suka iske an tone kabari babu gawar a ciki. Lamarin ya saka tashin hankali da fargaba a tsakanin mutanen dake zaune a kusa da makabartar inda suke kiran jami'an tsaro da gwamnatin jihar ta kai musu dauki.