
Babu ƙanshin gaskiya cewa sojojinmu na yin murabus – Rundunar sojin Najeriya
Rundunar Sojin Najeriya ta musanta rahotannin kafafen yaɗa labarai na baya-bayan nan da ke nuna cewa jami'anta sun yi murabus daga aikinsu ne saboda cin hanci da rashawa, da rashin ɗa’a, da kuma rashin walwala.
A makon nan ne dai wasu kafofin watsa labaran Najeriya suka yi ta naƙalto wani rahoto da ke nuna yadda sojoji fiye da guda 1000 suka yi murabus bisa zarge-zargen rashin jin daɗin aiki da rashawa da cin hanci "da ya yi wa aikin katutu".
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana waɗannan iƙirari a matsayin karya da kuma yunƙurin ɓata mata suna da gangan.
A cewar rundunar, rahotannin an yi su ne domin haifar da saɓani da kuma ɓata tarbiyar jami’anta.
Sanarwar ta kara da cewa: "Batun cewa sojoji na yin murabus daga muƙamansu saboda rashin jin dadin rayuwa, da cin...