
An koro ‘yan Arewa 114 guda daga jihar Ondo
Gwamnatin jihar Ondo dake kudancin Najeriya ta kamo 'yan Arewa su 114 da aka samu a dazukan jihar inda aka dawo dasu gida Arewa.
Hukumar jami'an tsaron Amotekun na jihar ne suka kama mutanen suka kuma taso keyarsu zuwa Arewa.
Kwamandan Amotekun din, Akogun Adetunji Adeleye ya bayyana cewa sun kama mutanen ne saboda sun tambayesu me ya kawosu dajin jihar amma in banda mutum uku a cikinsu, duka sun kasa fadin abinda ya kaisu jihar.
Ya kara da cewa, wadanda suka kaisu dazukan jihar a manyan motoci sun ce musu su bazama a daji ne nan gaba zasu sanar dasu abinda zasu yi.
Ya kara da cewa, Gwamnan jihar, Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa ya basu umarnin kama mutanen da mayar dasu Arewa.
Yace, tabbas kundin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa kowa damar yin walwala da zuwa inda yake so a f...