Tuesday, December 16
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Jami’an tsaro na gani wasu abubuwan ke faruwa amma sai suce wai ba zasu dauki mataki ba saboda suna jiran Umarni>>Inji Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare

Jami’an tsaro na gani wasu abubuwan ke faruwa amma sai suce wai ba zasu dauki mataki ba saboda suna jiran Umarni>>Inji Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare

Duk Labarai
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya bayar da labarin cewa, a wasu lokutan jami'an tsaro na kallo wasu abubuwan ke faruwa amma sai su ce wai ba zasu iya daukar mataki ba suna jiran umarni daga sama. Ya bayyana hakane yayin hira da manema labarai. Dauda yace wasu lokutan har kuka yake. Yace abin takaici duk inda wani shugaban 'yan Bindiga yake a jiharsa ya sani kuma duk inda zasu yana sane amma babu abinda zai iya yi. https://twitter.com/AM_Saleeeem/status/1963549967643034005?s=19
Ina goyon bayan Tinubu ya zarce a 2027, Kuma Kwankwaso ya mai mataimaki>>Inji Dan majalisa Abdulmumin Jibrin

Ina goyon bayan Tinubu ya zarce a 2027, Kuma Kwankwaso ya mai mataimaki>>Inji Dan majalisa Abdulmumin Jibrin

Duk Labarai
Dan majalisar tarayya daga jihar Kano, Abdulmumin Jibrin ya bayyana cewa, Yana goyon bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya zarce a shekarar 2027. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV. Yace dalilinsa shine yana son kamar yanda Arewa ta yi shekaru 8 akan mulki, itama kudu ta kammala shekaru 8. Yace yana mamakin dan Arewa ya rika cewa an cuci Arewa a tsarin karba-karba na mulki a Najeriya. https://twitter.com/Imranmuhdz/status/1963321987444424770?t=xvm4haloRuAuSdXvW_n7uQ&s=19
Kalli Bidiyo: Budurwa me wanke-wanke ta dauki hankula sosai inda da yawa ke cewa aikin bai dace da ita ba

Kalli Bidiyo: Budurwa me wanke-wanke ta dauki hankula sosai inda da yawa ke cewa aikin bai dace da ita ba

Duk Labarai
Wannan Budurwar me wanke wake a wajan sayar da abinci ta dauki hankula sosai inda da yawa ke cewa aikin bai dace da ita ba. Bidiyonta na ta yawo a kafafen sada zumunta inda da yawa ke yabawa ds kyawunta. https://twitter.com/The__Vyrus/status/1963238904951091348?t=RXudu-DZBYlJB9qB2Hl_vQ&s=19 Wani dai yace yana son a nemo mai ita.
Duk budurwar da Saurayi ya aika mata da kudin mota da niyyar cewa ta je ta sameshi amma ta ki zuwa zata iya fuskantar hukunci, Hukumar ‘yansandan Najeriya ta gargadi ‘yan mata

Duk budurwar da Saurayi ya aika mata da kudin mota da niyyar cewa ta je ta sameshi amma ta ki zuwa zata iya fuskantar hukunci, Hukumar ‘yansandan Najeriya ta gargadi ‘yan mata

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan Najeriya reshen jihar Rivers sun gargadi 'yan mata dake karbar kudin mota a hannub samari da niyyar cewa zasu je a hadu amma su ki zuwa. Hukumar tace hakan laifi ne na zamba cikin aminci da kuma samun kudi ta hanyar karya, hukumar tace idan saurayi ya shigar da kara, za'a iya hukunta budurwar. Kakakin 'yansandan jihar, Grace Iringe-Koko ce ta bayyana hakan a shafinta na X inda ta jawo hankalin mutane su daina neman kudi ta hanyar da bata dace ba.
Bidiyo Gwanin ban Sha’awa: Kalli Yanda kasar Yèmèn ta yi bikin murnar Haihuwar Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) da ya kayar sosai ake ta yabawa

Bidiyo Gwanin ban Sha’awa: Kalli Yanda kasar Yèmèn ta yi bikin murnar Haihuwar Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) da ya kayar sosai ake ta yabawa

Duk Labarai
Kasar Yemen ta yi bikin murnar haihuwar fiyayyen Halitta, Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ta hanyar mamaye babban birninta da kalar Shudi. An kuma rika harba wuta me kara da ake kira da fire works. Lamarin ya kayar sosai inda mutane ke ta yabawa. https://twitter.com/GlobeEyeNews/status/1963326598398317012?t=z6l4eNEV90CI7x2w-cJGTA&s=19 Allahumma Salli Ala Mohammad wa ala ali Muhammad, kama Sallaita Ala Ibrahim wa ala ali Ibrahim fil alamin Innaka hamidum majid Allahumma Barik ala Muhammad wa'ala Ali Muhammad kama barakta Ala Ibrahim wa ala ali Ibrahim innaka hamidummajid
Wannan wane irin hukunci ne? Kotu ta daure barawon doya wadda kudinta bai wuce Naira 35,000 shekaru 3 a gidan yari, da aiki me wahala, sanan babu zabin biyan tara

Wannan wane irin hukunci ne? Kotu ta daure barawon doya wadda kudinta bai wuce Naira 35,000 shekaru 3 a gidan yari, da aiki me wahala, sanan babu zabin biyan tara

Duk Labarai
Wani barawon dota me suna Akeem Jimoh dan kimanin shekaru 28 ya fuskanci hukuncin daurin shekaru 3 a gidan yari. Doyar da ya sata dai darajarta Naira dubu talatin da biyarne watau 35,000. Barawon dai ya amsa laifinsa bayan da aka gurfanar dashi a gaban kotu dake Osogbo jihar Osun. Yayi satar ne ranar Juma'a da misalin karfe 10 a watan July 25, 2025 kuma doyar da ya sata sanda 17 ce. Barawon dai bashi da lauya, kuma da aka tambayeshi dalilin yin wannan sata, yace yunwa ce ta sakashi hakan inda ya roki kotu ta tausaya masa. Sunan wanda akawa satar, Tiamiyu Abegunde. Rahoton yace me gabatar da kara Babatunde Olukokun yace Akeem Jimoh yace an taba yi mai daurin shekaru 3 a gidan yari bayan da ya tsayawa wani ya karbi belinsa amma wancan din ya tsere. Mai shari'a, Magistrat...
Kalli Bidiyon yanda shugaban kasar Iyran yaki amincewa ya gaisa da matar shugaban kasar China duk da ta mika masa hannu, hakanan ita matarsa taki amincewa ta gaisa da shugaban kasar Chinan saboda kishin Addini

Shugaban kasar Iran ya dauki hankula sosai a waja bikin zagayowar ranar samun 'yancin kasar China inda aka ga yaki amincewa ya gaisa da matar shugaban kasar Chinan duk da ta mika masa hannu. Hakan ya farune yayin da shugaban kasar Chinan yake musu maraba da isa kasar wajan bikin. Hakanan itama matarsa taki amincewa ta gaisa da shugaban kasar China din. Mutane da yawa sun musu addu'a da fatan Alheri dayawa kuma sun nuna jin dadinsu. https://twitter.com/A_M_R_M1/status/1963291632456937976?t=e5jjrFKB8lT5vu6_u4bEkQ&s=19 Lamarin ya kayaar sosai
Mun Chanja Tsarin Aiki: Daga yanzu karku sake jiran Umarni daga sama, duk inda aka kaiku aiki kuka ga ba daidai ba, ku saki WùUta kawai>>Shugaban Sojojin Najeriya, Christopher Musa

Mun Chanja Tsarin Aiki: Daga yanzu karku sake jiran Umarni daga sama, duk inda aka kaiku aiki kuka ga ba daidai ba, ku saki WùUta kawai>>Shugaban Sojojin Najeriya, Christopher Musa

Duk Labarai
Shugaban sojojin Najeriya, Christopher Musa ya baiwa sojojin Umarnin cewa duk inda aka kaisu aiki kada su sake jiran wai sai an basu umarnin yin harbi. Yace idan suka ga yankin da aka kaisu aiki na cikin barazana, su dauki mataki, idan suka ga gini ko ma'aikatar da aka kaisu aiki na cikin barazana su dauki mataki, idan suka ga abokin aikinsu na cikin barazana su dauki mataki hakanan idan suka samu kansu a cikin barazana su dauki mataki. Shugaban sojojin yace bai son wani soja ya kara bashi uzurin cewa wai an yi abinda bai dace ba a kusa dashi ko kuma an kai Hhàriy a kusa dashi bai dauki mataki ba yace masa wai saboda ba'a bashi umarni bane, yace kada sojojin su sake jiran umarni. Sannan ya gargadi kwamandojin sojojin da cewa duk wanda aka samu barakar aikata ba daidai ba a rundun...
Kalli Bidiyo: Sabuwar Wakar Yabon Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) da matar Rarara, Aishatulhumaira ta yi ta jawo cece-kuce inda wasu ke cewa ta yaya ta yi waka da wanda ba mijinta ba?

Kalli Bidiyo: Sabuwar Wakar Yabon Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) da matar Rarara, Aishatulhumaira ta yi ta jawo cece-kuce inda wasu ke cewa ta yaya ta yi waka da wanda ba mijinta ba?

Duk Labarai
Matar tauraron mawakin Siyasa, Dauda Kahutu Rarara watau, Hajiya Aishatulhumaira ta jawo cece-kuce bayan wallafa wakar yabon Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) da ta yi. Ta yi wakar ne tare da wani me suna Hafiz Abdallah inda ta nemi mutane su je shafinta na YouTube su kallah. Saidai yayin da wasu suka yaba, wasu kuwa sun bayyana cewa hakan bai dace ba. A baya dai an ga yanda Rarara da A'ishatulhumaira suke waka tare. Kalli Wakar anan