Saturday, December 13
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Ƴan Najeriya miliyan 31 na fuskantar matsalar ƙarancin abinci – MDD

Ƴan Najeriya miliyan 31 na fuskantar matsalar ƙarancin abinci – MDD

Duk Labarai
Ofishin hukumar kula da jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta nuna damuwa kan ƙaruwar yunwa da talauci da kuma rashin tsaro a Najeriya, inda ta yi kiyasin cewa ƴan ƙasar miliyan 31 na fama da matsalar ƙarancin abinci. Hukumar ta ce akwai sama da yara miliyan goma ƴan ƙasa da shekara biyar da ke fama da rashin abinci mai gina jiki. Bayanin haka ya fito ne a taron da gwamnatin tarayya da hukumar suka gudanar yayin bikin ranar Jin-Ƙai ta Duniya na 2025, wanda aka gudanar ranar Talata a Abuja, mai taken "ƙarfafa haɗin gwiwa a duniya da kuma tallafawa al'ummomi". Hukumar ta ce ya kamata a ɗauki matakai cikin gaggawa domin rage barazanar ƙaruwar matsalar. Jami'in hukumar ta jin-ƙai a Najeriya, Mohamed Fall, ya bayyana cewa bikin ranar ta bana ya zo ne a daidai lokacin da ake samun ra...
Zai yi wuya Kwankwaso ya marawa Tinubu baya a 2027 – Buba Galadima

Zai yi wuya Kwankwaso ya marawa Tinubu baya a 2027 – Buba Galadima

Duk Labarai
Zai yi wuya Kwankwaso ya marawa Tinubu baya a 2027 - Buba Galadima. Buba Galadima, jigo a jam’iyyar NNPP kuma na kusa da tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce zai yi matuƙar wuya Kwankwaso ya haɗa kai da jam’iyyar domin mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen 2027. Galadima ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels , inda ya zargi gwamnatin Tinubu da nuna adawa ga Kwankwaso ta hanyar goyon bayan Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, duk da cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta tsige shi. Ya ce Kwankwaso ba ya buƙatar dogaro da APC a siyasa, yana mai tunatar da cewa ya kayar da jam’iyyar a Kano a baya. “Kwankwaso bai taɓa gaya min cewa zai mara wa Tinubu baya a 2027 ba,” in ji shi. Galadima ya ƙar...
Gwamna Yusuf ya rantsar da sabon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano

Gwamna Yusuf ya rantsar da sabon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano

Duk Labarai
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da sabon shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da rashawa ta Kano, Barista Sa’idu Yahaya. An gudanar da bikin rantsuwar ne a fadar gwamnatin Kano ranar Laraba, inda Kwamishinan Shari’a na jihar, Barista Haruna Isa Dederi, ya jagoranci ɗaukar rantsuwar aiki. A ranar 1 ga watan Agusta, Gwamna Yusuf ya gabatar da sunan Barista Yahaya a matsayin sabon shugaban hukumar, sannan aka tura sunan nasa zuwa majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatarwa. Wannan nazuwa ne bayan ƙarewar wa’adin tsohon shugaban hukumar, Barista Muhuyi Magaji Rimingado. An haifi Yahaya a shekarar 1978, kuma ƙwararre ne a fannin yaƙi da cin hanci. Yana da digiri a tattalin arziki daga Jami’ar Bayero Kano (BUK) da kuma digirin dig...
Ji yanda Ɗaurarre a gidan yari ya lashe zaɓen cike-gurbi na majalisa a jihar Enugu

Ji yanda Ɗaurarre a gidan yari ya lashe zaɓen cike-gurbi na majalisa a jihar Enugu

Duk Labarai
Hukumar zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta bayyana wani ɗan gidan yari, Bright Ngene na jam'iyyar Labour da aka ɗaure saboda satar naira miliyan 15, a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Enugu ta kudu da aka yi a ƙarshen makon da ya gabata. Mai magana da yawun hukumar a jihar, Sam Olumekun ya gabatar da sakamakon, bayan soke wanda aka yi a 2023. RFI ya rawaito cewa a ranar 28 ga watan Yulin wannan shekara alkali ya ɗaure Ngene shekaru 7 a gidan yari, saboda samun sa da laifin satar naira miliyan 15 kuɗaɗen al'ummar yankin da ya fito da ke Jihar Enugu. Rahotanni sun ce ya aikata laifin ne tun a shekarar 2017, amma a lokacin alkali ya bada damar cewar a kai shari'ar hukumar sasanta al'umma. Amma bayan nasarar da ya samu a zaɓen shekarar 2023, sai alkalin ya ce an ba shi uma...
Cin Amana Ne Zaɓar Shugaban Da Bai Cancanta Ba, Cewar Sheikh Dr. Abdulƙadir Adam Isawa

Cin Amana Ne Zaɓar Shugaban Da Bai Cancanta Ba, Cewar Sheikh Dr. Abdulƙadir Adam Isawa

Duk Labarai
Cin Amana Ne Zaɓar Shugaban Da Bai Cancanta Ba, Cewar Sheikh Dr. Abdulƙadir Adam Isawa. Malamin ya bayyana haka ne a karatun littafin Sahihul Bukhari da aka yi zama na arba'in da tara kamar yadda aka saba gudanar da karatun a kowane mako a Masallacin Jami'urrahmah da ke unguwar Kundila a titin Maiduguri na Birnin Kano. Malamin ya nuna damuwa da takaicinsa kan yadda ake ruɗar mutane da kuɗi kalilan wajen zaɓar miyagun shugabannin da ba su cancanta ba. A ba ka kuɗin da za ka cinye a kwana ɗaya ka zaɓi wanda zai yi shekara huɗu yana azabtar da kai, inda Malamin ya ambaci hakan a matsayin cin amana, kuma hakan yana daga cikin alamomin tashin alƙiyama zaɓar shugabannin da ba su cancanta ba, kawai don sun bayar da taliya. Malamin ya yi karatu a babin da ya bayyana yadda wani Balarab...
Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kudi Naira Miliyan Dubu Domin Gina Makarantar Horar Da ‘Yan Sanda A Garin Kafin Hausa Dake Jigawa

Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kudi Naira Miliyan Dubu Domin Gina Makarantar Horar Da ‘Yan Sanda A Garin Kafin Hausa Dake Jigawa

Duk Labarai
Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin ‘yan sanda, Sanata Abdulhamid Ahmed Malam Madori, ne ya bayyana haka yayin taron gwamnati da jama-a a Kafin Hausa. Ya ce an sanya kudin a cikin kasafin kudin 2025, kuma majalisar dattawa ta riga ta amince da dokar kafa makarantar wadda ake jiran sa hannun shugaban kasa. Sanata Malam Madori ya bayyana cewa shi ne ya dauki nauyin gabatar da kudurin kafa makarantar wadda za ta taimaka wajen samar da kwararrun ‘yan sanda na zamani domin inganta harkar tsaro a fadin kasar nan. Ya nuna cewa ya riga ya bai wa ofishin ‘yan sanda na Kafin Hausa sabuwar motar Hilux tare da gyara da samar da kayayyaki ga ofishin da gidajen ‘yan sanda, domin karfafa gwiwar jami’an da ke aiki a yankin. Bugu da kari, ya tallafa wa matasa da mata sama da 8,000 a K...
Ku yi hattara da abinda kuke dorawa a kafafen sadarwa, yanzu Haka Gwamnati ta kulle shafuka Miliyan 13 da suka dora abubuwan da basu dacw ba a Soshiyal Midiya

Ku yi hattara da abinda kuke dorawa a kafafen sadarwa, yanzu Haka Gwamnati ta kulle shafuka Miliyan 13 da suka dora abubuwan da basu dacw ba a Soshiyal Midiya

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta sanar da kulle shafukan yanar gizo guda Miliyan 13 saboda dora abubuwan da basu dace ba. An kulle shafukan ne dake kan TikTok, Facebook, Instagram, and X, bayan da wadannan kafafe suka bada hadin kai wa Gwamnatin Najeriya wajan kai rahoton irin wannan shafukan. Wadannan shafukan sun sabawa dokar Najeriya wadda hukumomin Nigerian Communications Commission (NCC), the National Information Technology Development Agency (NITDA), da the National Broadcasting Commission (NBC) suka samar ta amfani da kafafen sada zumunta. Rahoton yace an goge shafukan ne dan tabbatar da ana tsaftace irin abubuwan da ake yadawa a kafafen sada zumunta. Wakiliyar Gwamnatin tarayya, Hajiya Umar ta jinjinawa kamfanonin sadarwar saboda bada hadin kai wajan goge irin wadannan shafukan.
Kalli Bidiyon yanda Ummi Nuhu ta yi kyau kwanaki kadan bayan da Hadiza Gabon ta yi hira da ita

Kalli Bidiyon yanda Ummi Nuhu ta yi kyau kwanaki kadan bayan da Hadiza Gabon ta yi hira da ita

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wani Bidiyon Ummi Nuhu ya bayyana inda aka ganta daya daga cikin masu shirya fina-finai yana hira da ita inda aka ga ta yi haske. A baya dai a lokacin da Hadiza Gabon ta yi hira da ita An ga Ummi Nuhu a wani hali na ban tausai inda daga baya rahotanni suka ce an hada mata kudaden tallafi. https://www.tiktok.com/@yakubu_producer/video/7539112872220101909?_t=ZS-8z2OYE8MRw8&_r=1 Da yawa dai sun yi mamakin ganin wannan Bidiyon inda suke tambayar shin sabon Bidiyon ne?
Abin Kunya: Kalli yanda aka bar Gurin da aka warewa Najeriya a taron kasashe dake gudana a Birnin Tokyo na kasar Japan ba kowa, yayin da sauran kasashen Duniya suke tsaye a wajen nasu

Abin Kunya: Kalli yanda aka bar Gurin da aka warewa Najeriya a taron kasashe dake gudana a Birnin Tokyo na kasar Japan ba kowa, yayin da sauran kasashen Duniya suke tsaye a wajen nasu

Duk Labarai
Wani dan Najeriya me suna Idris Ayo Bello ya bayyana yanda da ya halarci wajan taron ci gaban Afrika da aka gudanar a birnin Tokyo na kasar Japan da kuma abin kunyar da ya gani. Yace wajan da aka warewa Najeriya ta tsaya babu kowa a wajan. Yace da ya ga abin yayi yawa, shine da kansa ya je wajan ya tsaya ya kuma rika amsa tambayoyi akan kasuwancin Najeriya da ci gabanta da wasu 'yan kasashe ke yi. Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dai ya halarci wajan taron, kuma rahotanni sun bayyana cewa, an tanadi mutanen da zasu tsaya a irin wannan waje dan wakiltar Najeriya.