Dan majalisar dokoki na majalisar jihar Nasarawa, Musa Gude ya dauki hankula saboda nada masu taimaka masa guda 106
Dan majalisar wakilai na majalisar jihar Nasarawa, Musa Gude ya nada masu taimaka masa guda 106.
Ya bayyana hakane a hirar da yayi da kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN inda yace ya nada mutane 106 a matsayin masu taimaka masa ne dan ya tallafawa rayuwarsu.
Yace daga ciki akwai wadanda yake biya albashin Naira Dubu 10 har zuwa Dubu 100.
Dan majalisar wanda a jam'iyyar SDP yake daga mazabar Uke/Karshi yace ya tallafawa mutane a bangarori daban-daban da suka hada da Noma, ilimi, da sauransu.








