Da Duminsa: Gwamnati ta fitar da gargadin Ambaliyar ruwan da za’a kwashe kwanaki 5 ana yi a jihohi 19, karanta jadawalin Jihohin
Gwamnati tacw za'a kwashe kwanaki 5 ana ruwan sama a jere wanda hakan zai iya jawo ambaliyar ruwa a jihohi 19 da furare 76.
Bangaren kula da ambaliyar ruwa na ma'aikatar Muhalli ne ya fitar da wannan sanarwar.
Hakan na zuwane yayin da ambaliyar ruwan tuni ta shiga jihohin Gombe, Plateau, Ogun, Anambra, Delta, da Legas a ranar Talata.
Wannan ambaliyar ruwa a cewar sanarwar zata fara ne daga ranar 5 zuwa 9 ga watan Augusta.
Garuruwan da lamarin zai shafa sun hada da Akwa-Ibom (Edor, Eket, Ikom, Oron, Upenekang); Bauchi (Tafawa-Balewa, Azare, Jama’are, Kari, Misau, Jama’a); Ebonyi (Abakaliki, Echara, Ezilo); Cross-River (Ogoja Edor, Obubra); Nasarawa (Keana, Keffi, Wamba); Benue (Agaku, Buruku, Gboko, Igumale, Ito, Katsina-Ala, Ugba, Vande-Ikya); Kaduna (Jaji, Kafancha, Birnin-Gwa...








