Bayan Amarya Ta Gudu A Safiyar Ranar Daurin Aurensu, A Karshe Ango Ya Auri Daya Daga Cikin Kawayen Amarya A Ranar Auren
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya auku ne a garin Sabo-Ibadan dake jihar Oyo.
Me za ku ce?
A Yanzu Haka Za A Iya Biyan Naira Dubu Talatin A Matsayin Sadaki, Inji Limamin Masallacin Albabello Dake Zaria
Malamin ya ce "kamar yadda ya tabbata a mazhabar Imam Malik za a iya biyan rub'u dinar ko darhami uku, inda dubu talatin ce kiyasin darhami uku", Inji- Imam Dr. Hamza Assudaniy Babban Limamin Masallacin Juma'a Na Albabello Zaria.
Da Mu Da Kwankwaso Duk Tinubu Muka Yi Wa Aiki A Zaben 2023, Kuma Idan Har Kwankwason Da Na Sani Ne Zai Sake Sabunta Wannan Kwangilar A 2027, Inji Dan Bilki Kwamanda
Me za ku ce?
Wani rahoto da ya bayyana, ya nuna shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu a matsayin shugaba Mafi rashawa da cin hanci inda ya zo a matsayi na 3 a Duniya.
Wata kungiya me suna, (OCCRP) ce ta bayyana hakan.
Ta kuma samu wanna sakamako ne bayan da ta nemi a yi zabe dan fitar da mutane mafiya rashawa a Duniya.
Kungiyar ta hada da manyan 'yan Jarida ne da 'yan fafutuka dan kare hakkin al'umma. Shugban kasar Kenya, William Ruto ne ya zo na daya sai kuma shugaban kasar Indonesia, Joko Widodo ya zo na uku.
Hambararren Shugaban kasar Syria, Bashar al-Assad ne ya zamo gwarzon shekara.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, bai yi wata murna da zama shugaban kasa ba bayan da ya iske irin barnar da aka yiwa Najeriya.
A bayyana hakane ga kakakin majalisar dattijai, Godwill Akpabio.
Akpabio ne ya bayyana hakan a wajan rabon kayan da yayi ga mutanen mazabarsa wanda suka hada da kayan abinci da ababen hawa da sauransu a jiharsa ta Akwa-Ibom.
Yace wata rana ya taba tabayar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kan shin ko yayi murnar zama shugaban kasa kuwa lura da irin barnar da ya iske tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele yawa kasar?
Sai shugaba Tinubu yace masa murna kadan yayi. Bai san barnar da akawa Najeriya ta kai haka ba.
Akpabio ya kara da cewa, ya gayawa shugaban kasar cewa, yayi imanin kamar yanda ya gyara Legas, Itama Na...
Bincike ya nuna cewa, matasa dake tsakanin shekaru 21 zuwa 30 ne a Najeriya suka fi amfani da maganin karfin maza .
Yawanci ana sayen magungunan kara karfin maza ne dan samun kuzari da jin dadin jima'i.
Saidai da yawa daga cikin magungunan da ake sayarwa din basu da rijista hukukomin lafiya na kasa basu tantance su ba, hakanan kuma mafi yawan masu sayar da magungunan ma basu da ilimi akan harkar maganin.
Hakan yasa ake samun matsalar magungunan su rika bayar da illa ga lafiyar dan adam inda akan samu matsalar mazaje na mutuwa yayin jima'i.
Sanata Ali Ndume daga jihar Borno yayi kira ga sarakunan dake karkashin mazabarsa da kada su yadda da sabuwar dokar haraji ta shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Ya bayyana hakane a yayin da ya kai ziyara Masarautar Askira, inda yace dalilinsa na kin amincewa da dokar harajin shine wahalar da mutane ke ciki, dan hakane yake kira da sarakunan da suma kada su amince da ita.
Yayi kira ga matasa da su tashi su rungumi harkar noma inda yace a daina dogaro da gwamnati da Albashi dan kuwa albashin Naira dubu 70 ba zai sayi buhun shinkafa ba dake Naira dubu 100 ko buhun wake dake Neman kaiwa Naira dubu dari 200.
Ya jinjinawa mutanen garin Gwoza saboda jajircewar da suka nuna duk da matsalar tsaron da suke fama da ita inda yace babu yanda za'a yi a rika kawo musu hare-hare ba tare da masu b...
Tsohon kakakin majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawal ya bayyana cewa, mutane na cikin matsin rayuwa kuma rabon kayan abinci ba shi bane mafita.
Ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar ta bakin kakakinsa, Ezrel Tabiowo bayan da ya je mazabarsa dake jihar Yobe ya raba kayan tallafi.
Yace kamata yayi a samarwa mutane hanya da zasu dogara da kansu amma rabon abinci zai kawo sauki ne kawai na dan lokaci wanda kuma wahalar zata ci gaba.
Saidai yace kamin su kai ga wancan matsayi, su dake da halin bayarwa zasu ci gaba da bada tallafin dan saukakawa mutane rayuwa.
Yayi kira ga masu rike da madafan iko dasu dauki matakan da zasu kawowa Al'umma saukin rayuwa.
Biyo bayan fara dawo da ci gaba da aikin matatar man fetur ta Warri, 'yan kasuwar man fetur sun bayyana kyakykyawan zatom cewa, farashin man fetur din zai sauka.
'Yan kasuwar sun ce yanzu gasa tsakanin masu matatun man fetur na cikin gida zata yi tsanani ta yanda dole za'a sauke farashin man fetur din.
Sun bayyana hakane ranar Litinin bayan fara aikin matatar man fetur ta Warri.
Kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya bayyana cewa, zai fara fitar da man fetur din zuwa kasashen waje dan samun kudin shiga.
Hakan na zuwane wata daya bayan da matatar man fetur da Fatakwal ta fara aiki.