Tuesday, May 13
Shadow

Author: Auwal Abubakar

Gwamnan Abia ya Karrama Kwankwaso kan yadda Ya Gina Al’umma a rayuwarsa

Gwamnan Abia ya Karrama Kwankwaso kan yadda Ya Gina Al’umma a rayuwarsa

Duk Labarai
Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya karbi bakuncin Jagoran jam'iyyar NNPP na kasa Sen. Rabi'u Musa Kwankwaso a gidan gwamnati dake Umuahia. Tattaunawar tasu ta ta'allaka ne kan siyasar kasa da kuma makomar Najeriya. A wani biki na musamman wanda Gwamna Otti ya karrama Sanata Kwankwaso da lambar yabo kan irin gudunmawar da ya bayar ga al’umma, a zamaninsa na Mulki da kuma bayan Mulki. Saifullahi Hassan
Cire tallafin Man fetur ne abu mafi kyau da armashi da ya faru da Najeriya>>Inji Sanata Sani Musa

Cire tallafin Man fetur ne abu mafi kyau da armashi da ya faru da Najeriya>>Inji Sanata Sani Musa

Duk Labarai
Sanata Sani Musa wanda shine shugaban kwamitin dake kula da kudi a majalisar tarayya ya bayyana cewa, cire tallafin man fetur ne abu mafi kyau da ya faru da Najeriya. Yace hakan zai bayar da damar yanayin kasuwa ya bayyana farashin man fetur din. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV inda yace wannan mataki zai bayar da damar raba arzikin gwamnati yanda ya kamata. Yace idan dai kudaden da ake turawa Gwamnoni suna aiki dasu yanda ya kamata, za'a samu ci gaba sosai. Yace cire tallafin zai sa gwamnati ta samu karin kudin shiga ta yanda zata rika kashe kudaden nata ta hanyar da ya dace.
Kada ku ga Jam’iyyar Adawa ta kayar da jam’iyya me mulki a kasar Amurka, a Najeriya hakan ba zai faru ba, Tinubu ne zai sake cin zabe a 2027>>Inji Jam’iyyar APC

Kada ku ga Jam’iyyar Adawa ta kayar da jam’iyya me mulki a kasar Amurka, a Najeriya hakan ba zai faru ba, Tinubu ne zai sake cin zabe a 2027>>Inji Jam’iyyar APC

Duk Labarai
Jam'iyyar APC me mulki a Najeriya ta gargadi jam'iyyun Adawa da cewa kada su ga jam'iyyar Adawa a kasar Amurka ta kayar da jam'iyya me mulki, A Najeriya hakan ba zai faru ba. APC ta kara da cewa, Tinubu ne zai lashe zaben shugaban kasa a Najeriya a zaben shekarar 2027. A kasar Amurka dai 'yar takara jam'iyya me mulki ta Democrat, Kamala Harris ta sha kaye a hannun dan takarar jam'iyyar Adawa ta Republic, Donald Trump wanda shine ya sake zama shugaban kasa a karo na biyu. Jam'iyyun Labour party dana NNPP sun bayyana hakan da abin nasara wanda suka ce ya kamata hukumar zabe me zaman kanta INEC ta koyi darasi daga zaben. Saidai a martanin jam'iyya me mulki a Najeriya ta APC ta bakin kakakinta, Bala Ibrahim ta bayyana cewa, hakan ba zai faru ba a Najeriya dan kuwa shugaban kasa, Bo...
Kungiyar Masu Hako danyen Man fetur a Najeriya sun gargadi Gwamnati akan baiwa ‘yan kasuwa lasisin shigo da man fetur Najeriya

Kungiyar Masu Hako danyen Man fetur a Najeriya sun gargadi Gwamnati akan baiwa ‘yan kasuwa lasisin shigo da man fetur Najeriya

Duk Labarai
Kungiyar kamfanonin dake hako danyen man fetur a Najeriya, CORAN ta gargadi Gwamnatin tarayya ta yi hankali da baiwa 'yan kasuwa lasisin shigo da man fetur daga kasashen waje. Hakan na zuwane a yayin da baraka ta faru tsakanin 'yan kasuwar da Matatar man fetur ta Dangote inda aka shiga kotu, 'yan kasuwar na neman a basu lasisin shigo da man fetur din daga kasar waje saboda sun ce man fetur din Dangote yayi tsada amma shi kuma yana neman kada a basu lasisin saboda a cewarsa zasu shigo da man fetur din da bai da inganci wanda gurbataccene. A sanarwar da kungiyar CORAN ta fitar ta bakin Sakataren yada labaranta, Eche Idoko tace abin damuwa ne yanda 'yan kasuwar suka nace sai sun shigo da man fetur din daga kasar waje. Yace 'yan kasuwar suna son mayar da Najeriya wajan kawo man fetur ...
Ku daina Rige-Rigen zuwa kasashen waje neman aiki, Ku tsaya mu gyara kasa>>Shugaba Tinibu ya roki Matasa

Ku daina Rige-Rigen zuwa kasashen waje neman aiki, Ku tsaya mu gyara kasa>>Shugaba Tinibu ya roki Matasa

Duk Labarai
Shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu ya roki matasan Najeriya da su daina rige-rigen fita kasashen waje neman aiki. Shugaban ya roki matasa da su tsaya a gyara kasa dan kuwa Najeriya ma zata iya zama kamar kasashen da suke mafarkin zuwa. Tinubu ya bayyana hakane a wajan taron yaye daliban Jami'ar Uyo inda shugaban jami'ar Port Harcourt, Prof. Owunari Georgewill ya wakilceshi. Ya jawo hankalin matasan akan su yi amfani da ilimin da suke dashi wajan warware matsalolin da ake dasu a Najeriya.
Yawan ‘yan Najeriya dake daukar Albashin kasa da Dubu 100 sun karu

Yawan ‘yan Najeriya dake daukar Albashin kasa da Dubu 100 sun karu

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa yawan 'yan Najeriya dake daukar Albashin kasa da Naira Dubu 100 sun kai kaso 42 cikin 100. Saidai a shekarar data gabata ta 2023,mutanen da suke karbar albashin kasa da dubu 100 a wata kaso 26 ne. Hakanan faduwar darajar Naira tasa 'yan Najeriyar masu daukar kasa da Naira dubu 100 suke shan wahala wajan biyan bukatansu na yau da kullun Hakanan wanda basu da hanyar samun kudi a yanzu aun kari zuwa kaso 28 cikin 100.