Monday, December 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Akwai alkawarin cewa Obasanjo Atiku zai baiwa mulki idan ya kammala amma yaci Amanarsa>>InJi Dele Momodu, ji yanda lamarin ya faru

Akwai alkawarin cewa Obasanjo Atiku zai baiwa mulki idan ya kammala amma yaci Amanarsa>>InJi Dele Momodu, ji yanda lamarin ya faru

Duk Labarai
Mawallafin jaridar Ovation Magazine, Dele Momodu ya bayyana cewa, akwai alkawari tsakanin Atiku Abubakar da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo kan cewa, Obasanjo zai yi mulkin wa'adi daya ne ya sauka ya baiwa Atikun. Saidai Obasanjo be cika wannan alkawari ba. Dele Momodu yace duk da wannan Atiku bai daina baiwa Obasanjo girmansa ba duk da cewa yana da goyon bayan gwamnoni a wancan lokacin. Dele Momodu yace daga karshema Obasanjo sawa yayi aka kwace abubuwan da kundin tsarin mulki suka tanada a baiwa Atiku. Yace amma Atiku sai ya mayar da hankali akan kasuwanci, kuma yayi ta samun ci gaba, yace da sauran 'yan siyasa sun kasance irin Atiku masu sana'a da Najeriya bata samu kanta a halin da take ciki yanzu ba.
‘Yan Najeriya basu taba shan wahalar da suke sha a Gwamnatin Tinubu ba>>Inji Sanata Dino Melaye

‘Yan Najeriya basu taba shan wahalar da suke sha a Gwamnatin Tinubu ba>>Inji Sanata Dino Melaye

Duk Labarai
Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa 'yan Najeriya basu taba shan irin wahalar da suke sha a gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channels TV. Yace wasu har bola suke bi suna tsintar Abinci. Melaye yace mutum idan yana son ya gane irin wahalar da ake ciki, ya je kauye, mutane na ta mutuwa saboda tsananin rashin abinci. Da yake magana akan jam'iyyar PDP, Sanata Dino Melaye yace APC ta rika ta saye jam'iyyar PDP da hakan PDP ba jam'iyyar dogaro bace.
Kalli Bidiyo:Babbar Matsalar Ummi Nuhu shaye-shaye ne har makaranta sai da ta shiga amma aka koreta saboda matsalar>>Inji Shagari Shaggy

Kalli Bidiyo:Babbar Matsalar Ummi Nuhu shaye-shaye ne har makaranta sai da ta shiga amma aka koreta saboda matsalar>>Inji Shagari Shaggy

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Shagari Shaggy wanda yace shi abokin Ummi Nuhu ne lokacin tana ganiyarta, yace Ummi Nuhu a wancan lokacin tana da motoci 2 da gwala-gwalai da fili. Yace amma duk ta sayar dasu ta kama shaye-shaye. A cewarsa, Babu abinda Ummi Bata sha har gungun 'yan shaye-shaye take bi. https://www.tiktok.com/@shagarishaggiy/video/7532102035953421624?_t=ZS-8yXSXwHRCyX&_r=1
Ji ABIN A YABA: Wani Hakimi A Jihar Bauchi Ya Siyo Masara Ya Karya Farashinta Daga Naira 700 Zuwa 450 Domin Saukakawa Mabukata

Ji ABIN A YABA: Wani Hakimi A Jihar Bauchi Ya Siyo Masara Ya Karya Farashinta Daga Naira 700 Zuwa 450 Domin Saukakawa Mabukata

Duk Labarai
ABIN A YABA: Wani Hakimi A Jihar Bauchi Ya Siyo Masara Ya Karya Farashinta Daga Naira 700 Zuwa 450 Domin Saukakawa Mabukata. Wani bawan Allah Hakimin kasar Ciroma ta Masarautan Misau dake jihar Bauchi, Alh Amadun Amadu ne ya karya farashin masara daga naira 700 da ake siyarwa a kasuwa zuwa naira 450. Hakimin ya siyo masarar ce da kudin sa domin saukaka mabukata su siya cikin farashi mai sauki. Ana siyar da masarar ne a kofar gidansa, kuma ya ce daga nan har zuwa wata guda za a cigaba da kawo masarar ana siyarwa da mabukata. Wace fata za ku yi wa wannan bawan Allah Alh Amadun Amadu? Daga Mohammed Sale Gariyo Misau
An kama matashi a jihar Katsina saboda yin zanga-zangar matsalar tsaro

An kama matashi a jihar Katsina saboda yin zanga-zangar matsalar tsaro

Duk Labarai
Hukumomi a jihar Katsina sun kama matashi me suna  Anas Muhammad Game saboda yayi zanga-zanga kan matsalar tsaron dake damun jihar. An kamashi ne kwanaki 6 da suka gabata a wajan zanga-zangar lumana ta nuna rashin jin dadin matsalar tsaron dake damun jihar. Tun wancan lokacin dai Muhammad Game ke tsare ba tare da Beli ba. Da yawa sun hau kafafen sada zumunta inda suke Allah wadai da ci gaba da tsareshi da neman a sakeshi da gaggawa.
Karin Baraka ta kunno kai a jam’iyyar ADC, inda dan majalisa, Leke Abejide yace shima bai yadda da su El-Rufai da Atiku a jam’iyyar ba

Karin Baraka ta kunno kai a jam’iyyar ADC, inda dan majalisa, Leke Abejide yace shima bai yadda da su El-Rufai da Atiku a jam’iyyar ba

Duk Labarai
Dan majalisar tarayya karkashin jam'iyyar ADC, Leke Abejide ya bayyana cewa ba zasu bar jam'iyyar su a hannun baki ba da suka musu kaka gida ba. Yace zai hada kai da 'yan Asalin jam'iyyar ADC din dan su kwato jam'iyyar daga hannun wanda suka musu kaka gida. Hakan na zuwane kwana daya bayan da tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa, Nafiu Bala daga jihar Gombe ya bayyana kansa a matsayin sabon shugaban jam'iyyar na kasa na riko. A wani labarin me kama da wannan, Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya bayyana cewa ba zai koma jam'iyyar ADC ba.
Kalli Bidiyo: Ko ka yadda ko baka yadda ba, Bola Ahmad Tinubu shine Shugaban kasa kuma shine ja gaba>>Inji Sheikh Kabir Gombe

Kalli Bidiyo: Ko ka yadda ko baka yadda ba, Bola Ahmad Tinubu shine Shugaban kasa kuma shine ja gaba>>Inji Sheikh Kabir Gombe

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Sheikh Kabir Gombe ya bayyana cewa a lokacin da aka kirkiri Najeriya, baya tsammanin shugaba kasa, Bola Ahmad Tinubu ya balaga. Ya bayyana cewa amma kuma yanzu shine shugaban kasa, Shine Ja gaba ko ka yadda ko baka yadda ba. Malam ya bayyana cewa, dole a hakura sai sanda mulkinsa ya kare. Ya kawo wannan misali ne ga wasu malaman darika a baya dake cewa su yarane da suke sukar Darika. https://www.tiktok.com/@saleemyusufmuhammadsambo/video/7533765736884391224?_t=ZS-8yXIaBqYGGX&_r=1
Kalli Bidiyo: ‘Yan Kannywood sun fi min Shehunan Darika irin su Inyasi da Shehu Tijjani Daraja>>Inji Malam Ibrahim Matayassara

Kalli Bidiyo: ‘Yan Kannywood sun fi min Shehunan Darika irin su Inyasi da Shehu Tijjani Daraja>>Inji Malam Ibrahim Matayassara

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Ibrahim Matayassara ya bayyana cewa, 'yan nanaye na Kannywood sun fi masa Shehunan Darika. Ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa dake ta yawo a kaffen sada zumunta. Malam yace kuma Marigayi, Sheikh Abubakar Mahmood Gumi yafi sauran manyan Shehunan Darika. https://www.tiktok.com/@assiddiqassalafyrlemo/video/7533755445920435462?_t=ZS-8yXH43efOxF&_r=1