
Ku Daina Abinda kuke ko mu yi maganinku dan kuwa babu wanda ke ja da Shugaba Tinubu yayi nasara>>Me baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro Malam Nuhu Ribadu ya gargadi ‘yan tà’àddàn Làkùràwà
Mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya ce gwamnatin shugaba Bola Tinubu za ta tabbatar da kawo ƙarshen ƙungiyar 'yan ta’adda da ake kira ‘Lukarawa’ a shiyyar Arewa maso yammacin nan ba da jimawa ba.
Ribadu ya bayyana haka ne a lokacin da ya wakilci shugaban kasa Tinubu a wajen bikin buɗe babban taron kwastam na shekarar 2024, ranar Laraba, a Abuja.
“Za mu fatattaki waɗanda ake kira Lukarawa daga kasarmu. Za mu kunyata masu sukar mu kuma zamu rufe bakunansu.
"Boko Haram da suka addabi kasarmu a baya, yanzu tserewa suke yi. Yanzu haka mambobinta suna tafiya zuwa wasu ƙasashe makwabta saboda ba su da damar yin ta’addancinsu a Najeriya” inji shi.
https://www.youtube.com/watch?v=cCxUX2BCOoA?si=5w06T_6XCLKlPcbM
Ya kuma bayyana cewa, alamun na ƙ...