Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour party a zaben shekarar 2023, Peter Obi ya kaiwa tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ziyara a gidansa dake Abuja.
Tsohon hadimin shugaban kasa, Hakeem Baba Ahmad ya baiwa Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar shawarar cewa, kamata yayi ya hakura da tsayawa takara a zaben 2027.
Hakeem yace Amaechi ma kamata yayi ya hakura.
Yace El-Rufai idan zai iya sai ya tsaya takarar.
Bayan bayyanar hirar da Hadiza Gabon ta yi da tsohuwar jarumar fina-finan Hausa, Ummi Nuhu inda aka ganta tana kuka tana bayar da labarin irin jarabawar data tsinci kanta a ciki, mutane da yawa sun tausaya mata.
Da yawa musamman mata, sun koka da hawaye bisa irin halin da suka ga tsohuwar jarumar a ciki.
Da yawa sun dora Bidiyon su suna kuka wasu kuma na kiran a tallafawa Ummi Nuhu:
https://www.tiktok.com/@iya_habu/video/7530991161511562501?_t=ZM-8yKQVh3VkmL&_r=1
https://www.tiktok.com/@officielhassanmakeup227/video/7530979471470365958?_t=ZM-8yKQam1m6tC&_r=1
https://www.tiktok.com/@hawee_maiduguri/video/7530943228003044609?_t=ZM-8yKQeS1dwW5&_r=1
Jam'iyyar SDP ta sanar da koran tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai tare da barrata kanta ga dukkan wasu lamuransa na siyasa da zai ambaci jam'iyyar.
Me ku ke gani a matsayin dalilin da ya sa jam'iyyar ta yi masa haka?
Wannan wata matashiyace da iyayenta ke ta shan yabo sosai a kafafen sada zumunta bayan abinda da aikata.
Yarinyar dai taki amincewa ne abokin karatunta ya mata rubutu a jikin kayan ta irin wanda ake yi dinnan bayan an kammala karatu.
Da ya takura sai ya mata a karshw ta falla masa mari.
https://www.tiktok.com/@binsadeeq02/video/7530645650904468758?_t=ZM-8yKOHOAdN4y&_r=1
Da yawa sun jinjina mata sosai, har wani ya mata kyautar kudi.
Malamin Addinin Islama, Ibrahim Matayassara ya bayyana cewa, Aske gashin hammata yafi Maulidi Daraja.
Malamin ya bayyana hakane a wani Bidiyo sa da ya watsu sosai a kafafen sadarwa.
Yace dalili kuwa shine ga babin Aske gashin hammata yazo a karatu amma babin Maulidi be zo ba.
https://www.tiktok.com/@ibrahimmatayassara/video/7530911491805990149?_t=ZM-8yKN1MpBHza&_r=1
Shugaban kasar Gambia, Adama Barrow ya je gaisuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari Daura.
Adama Barrow da tawagarsa sun je kabarin Buhari inda suka masa addu'a neman Rahama a wajan Allah.
Hadimin tsohon shugaban kasar, Malam Bashir Ahmad ne ya bayyana haka.
https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1948764520152793587?t=RHRnFLj-ou77bjl869PRWA&s=19
Ƴansandan Najeriya reshen Jihar Jigawa sun ce sun kama wani mutum mai suna Iliyasu Musa, ɗan shekara 40, bisa zargin kashe tsohuwar matarsa Hadiza Sale, ƴar shekara 30, a ƙauyen Afasha da ke ƙaramar hukumar Aujara.
Wanda ake zargin ya shafe sama da makonni biyu yana ɓuya tun bayan da lamarin ya faru a ranar 10 ga Yuli, 2025.
Ana zargin mutumin da kashe matar ne ta yin amfani da sanda sa'ilin da take kan hanyar komawa gida bayan ta dawo daga kasuwa da daddare.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, kakakinta SP Shi'isu Lawan Adam ya bayyana cewa jami’an ‘yansanda daga ofishin Aujara ne suka samu nasarar kama shi a ranar Talata, 23 ga Yuli, 2025 a ƙauyen Larabar-Tambarin-Gwani bayan tsantsan bibiyarsa da suka yi da kuma tura jami’ai na musamman don gano inda yake ɓuya.,
Rundu...
Hukumomi a Najeriya sun ce sun fara ƙoƙarin mayar da wasu ‘yan kasar da suka maƙale kuma suke gararamba a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya zuwa gida.
Wannan na zuwa ne bayan wani bidiyo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda aka yi watsi da mutanen cikin mawuyacin hali a yankin Bambari mai nisan kilomita 850 daga Bangui babban birnin kasar.
Wata sanarwa da Ma'iaktar Harkokin Wajen Najeriya ta fitar ta ce tuni ofishin jakadancin ƙasar a Bangui ya tuntuɓi mutanen.
"An karɓo fasfunansu kuma an tura motar da za ta ɗauko su daga Bambara zuwa Bangui," a cewar sanarwar.
"Ana sa ran za su isa Bangui bisa rakiyar jami'an tsaro a ranar Asabar."
Hukumar hana yiwa tattalin arziki kasa zagon kasa, EFCC ta tabbatar da hukuncin daurin watanni 5 da akawa jarumin Tiktok, Gfresh da Mawaki, Hamisu Breaker saboda wulakanta takardar Naira.
Hukumar tace duka su biyun bayan da aka karanto musu laifukansu sun amince basu yi gaddama ba.
Babbar kotun tarayya da ke jihar Kano a arewacin Najeriya ta ɗaure shahararrun mawaƙa Hamisu Breaker da G Fresh a gidan yari saboda kama su da laifin wulaƙanta takardun kuɗi na naira.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ce ta gurfanar da su a kotun, inda ta tuhumi Hamisu Sa'id Yusuf (Breaker) da Abubakar Ibrahim (G Fresh) da yin liƙin kuɗi yayin wasu bukukuwa.
Cikin rahoton daEFCC ta fitar, kotun ta kama G Fresh da laifin "liƙawa da kuma tattaka takardun kuɗi na N1,000 da suka kai N14,000" a...