Shahararren mawakin Najeriya, 2face Idibia ya bayyana cewa, mace daya tawa namiji kadan.
Yace mutum zai iya soyayya da mace daya amma ba zata iya biya masa bukatar sh'awarsa ba.
https://www.youtube.com/watch?v=jU9m-fDNMt0?si=zDa3SMdFeYq1nkfq
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi.
Wani dan Najeriya ya fashe da kuka bayan da budurwarsa ta ki daukar wayarsa.
Mutumin ya dawo daga kasar waje ne inda yayi ta neman Budurwarsa amma taki daga masa waya.
https://twitter.com/AsakyGRN/status/1939948404638937239?t=2V2tTU0ii9B8XRbjZTbONA&s=19
Dalili kenan ya fashe da kuka kuma ya dauki Bidiyo yake yadawa a kafafen sada zumunta.
Zan tsaya takarar shugaban kasa a 2027 – Peter Obi.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a zaben 2023, Peter Obi, ya tabbatar wa magoya bayansa cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027, kuma ba zai yi fiye da wa’adi guda ba idan ya ci zabe.
Mista Obi ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Peter Obi Media Reports, Ibrahim Umar, ya fitar a ranar Litinin a Abuja.
Tsohon dan takarar shugaban kasar ya tabbatar da cewa yana cikin tattaunawar kafa kawancen jam’iyyu, yana mai cewa burinsa shi ne ceton Najeriya daga halin da ta tsinci kanta.
“Ban taba shiga wata tattaunawa kan hadin gwiwar tikitin takara da kowa ba, har da Atiku,” inji shi.
“Idan za a samu wata yarjejeniya da za ta takaita wa’adin mulkina zuwa shekaru hudu...
Kakanninmu asali ƴan Najeriya ne – Shugabar Majalisar Dattawan Saint Lucia ta shaida wa Tinubu.
Shugabar Majalisar Dattawan kasar Saint Lucia, Alvina Reynolds, ta bayyana karfin alaƙa ta asali tun kakanni tsakanin ƙasar da Najeriya.
Reynolds ta buga misali da bayanan ƙidayar al'umma na Biritaniya da aka gudanar a tsibirin a 1815, inda aka gano cewa yawancin mutanen Saint Lucia na da asali daga Najeriya.
Ta bayyana hakan ne yayin tarbar Shugaba Bola Tinubu a zama na hadin gwiwa na majalisun dokoki biyu na kasar Saint Lucia a jiya Litinin.
Bayani game da wannan zaman hadin gwiwa, ta fito ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar ga manema labarai a jiya Litinin a birnin Abuja.
“Daga cikin bayi 16,282 da aka kawo Saint Lucia a waccan shek...
An gurfanar da matashin da ya hau kan allon talla saboda dan Tiktok a kotu.
Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano ta gurfanar da wani matashi mai shekaru 19 mai suna Ibrahim Abubakar, bisa laifin yunkurin kashe kansa, bayan da ya hau wata babban karfen talla a Kano ya kuma yi barazanar yin tsalle daga sama, yana danganta hakan da rashin ganin fitattun taurarin TikTok da yake kauna.
Abubakar, dan asalin jihar Adamawa, ya tayar da hankula a ranar Litinin a Gadar Lado da ke kan titin Zariya, lokacin da ya hau saman wani Babban allon talla ya kuma yi ikirarin zai kashe kansa idan har fitattun masu TikTok da yake bibiyarsu ba su bayyana a wurin ba.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a, Jami’in Hulda da Jama’a na ‘Yansanda a jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar d...
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya raka gawar kawunsa, Aminu Dantata daga Abu Dhabi kasar UAE zuwa Birnin Madina na kasar Saudiyya.
Aminu Dantata ne daya daga cikin kawun Dangote Dangote na karshe da suka rage masa.
https://twitter.com/SasDantata/status/1939963458931376381?t=OVEul28Z6bHYsZCZFuO5rw&s=19
Bayan sallar la'asar a kasar Saudiyya da misalin karfe 1:30 a Najeriya ne za'a yi jana'izar Marigayin.
Bayan sallar La'asar a ranar Talata ne ake sa ran za a gudanar da jana'izar fitaccen attajirin nan Alhaji Aminu Ɗantata a masallacin Madina.
Mustapha Junaid, mataimaki na musamman ga marigayin ya shaida wa BBC cewa shirye-shirye sun kammala domin gudanar da jana'izar.
"Alhamdu lillah an ɗauki marigayi Alhaji Aminu Ɗantata daga filin jirgi na Madina kuma yanzu haka za a je Shakzura inda a nan ne za a ƙarasa shirya shi kafin daga bisani a kai shi haramin Madina domin gudanar da sallah kamar yadda hukumomin Saudiyya suka amince." In ji Mustapha Junaid.
A ranar Asabar ne shahararren ɗankasuwa Aminu Ɗantata ya rasu yana da shekara 94 da haihuwa a shekarar miladiyya.
A shekarar Hijira (ta Musulunci) kuma, ya rasu yana da shekara 97, kamar yadda sakatarensa Mustapha Abdullahi ya shaid...
Rahotanni nata yawo a kafafen sada zumunta inda ake yada cewa, sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ne zai yiwa gawar Marigayi Aminu Dantata Sallah a birnin Madina.
Hakan na zuwane yayin da rahotanni ke cewa, Sarki Aminu Ado Bayero ma yace Santata ya bar masa wasiyyar cewa shine zai masa sallah.
A yanzu dai gawar marigayi Aminu Dantata ta isa Birnin Madina kuma ana jiran mahukunta birnin ne su bayyana lokacin da za'a masa sallah.
A hukumance, ba'a sanar da wanene zaiwa gawar Marigayi Aminu Dantata Sallah ba.
Rahotanni daga Madina birnin Ma'aiki na cewa, gawar marigayi Aminu Dantata ta isa birnin.
Bayan Saukar Gawar Marigayi Alh Aminu Dantata Tareda da Iyalensa; Alh Tajudeen Dantata da Hassan Dantata da Yaya, Jikoki da Yan Uwa Da Abokan Arziki duk Suna Wannan Guri Domin Mika Marigayi zuwa ga Ma'aikatan Kula Da Makabartar Baki'ah Inda akesa Rai Zasuyi masa Suttura. Allah yajikan sa Da Rahma.
https://twitter.com/GASHASHCOLLECT2/status/1939964376754057576?t=i0_KkOxpnECK4Dy5VN-ZiQ&s=19
Me magana da yawunsa yace zasu jira hukumomin Madina au basu lokacin da za'a masa sallah.