Wani Hincike ya bayyana kasashen da suka fi yawan mata masu manyan Nonuwa a Duniya.
Kasashen Guda 40 sun farane da kasar Norway a matsayin ta daya sai Amurka ta zo ta biyu sai Ingila tazo na 3.
Najeriya dai tazo ne a ta 39
!A yayin da shirye-Shirye suka yi nisa kan cewa, Abba Kabir Yusuf, gwamnan Kano da aka fi sani da Abba Gida-Gida na shirin komawa jam'iyyar APC.
Shi kuma jagoran Tafiyar Kwankwasiyya, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso na shirin komawa jam'iyyar ADC.
Kafar Thisday tace Kwankwaso na tattaunawa da jam'iyyar ADC inda yake shirin hadewa da su Atiku da Obi.
Dama dai Atiku ne yazo na 2 inda Obi ya zo na 3, Kwankwaso kuma ya zo na 4 a zaben shugaban kasa na shekarar 2023 da ya gabata.
Ana tsammanin idan wadannan manyan 'yan Adawa suka hade waje daya duk da cewa jam'iyya me mulki na da gwamnoni 28 zasu iya bata wuta.
'Yan kwankwasiyya Bangaren Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf sun fito da sabuwar Hula me nuna cewa suna tare da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
An ga Jar Hular me dauke da Tambarin Tinubu a jiki tana yawo a kafafen sada zumunta.
Hakan na zuwane yayin da Rahotanni suka ce ranar Litinin Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf zai koma jam'iyyar APC.
Tauraron mawakin Arewa, Soja Boy ya bayyana cewa, mahaifiyarsa bata yi Boko ba, shiyasa ma duk abinda aka kai mata yana yi sai yace mata karyane.
Soja Boy yace duk 'yan uwansa yayi Blocking dinsu Mahaifiyarsa ce kadai ta rage yake magana da ita.
Yace dalili suna ta gaya masa cewa abinda yake ba kyau.
Yace akwai inda yake son kaiwa kuma zai kai kamin ya mutu zai daina.
https://www.tiktok.com/@sojaboygarkuwayanarewa/video/7590765878594129163?_t=ZS-92lCSlKFAOX&_r=1
Rahotanni daga matatar man Dangote tace an dakatar da aiki a bangaren tace man fetur na matatar.
Hakan na zuwane daga bakin mataimakin shugaban kamfanonin Dangote me suna Devakumar Edwin wanda yace an dakatar da aikinne dan wasu 'yan Gyare-Gyare.
Yace idan aka kammala gyaran yawan man fetur din da matatar ke tacewa zai karu daga ganga 650,000 kullun zuwa ganga 700,000 kullun.
Wannan dalili yasa tuni Depot dake sayarwa da 'yan kasuwa man fetur suka kara farashin man su zuwa Naira 800 akan kowace lita.
Wannan matashiyar me yin Tiktok na ta fitowa tana bayyana cewa tana neman Mijin aure.
Kusan duka Bidiyon ta akan neman mijin aurene.
https://www.tiktok.com/@stargirl___131/video/7590718569961229586?_t=ZS-92l7qwDrcOn&_r=1
Tauraruwar fina-finan Hausa, ta bayyana cewa, ta bar harkar film saboda ba riba.
Tace shekarunta 20 tana harkar film amma bata ajiye komai ba.
Ta bayyana cewa yawanci dubu 5 ake biyansu idan suka yi fim.
Ta kara da cewa, yanzu haka bata da inda zata zauna sannan bata da sutura kuma abinci ma yana musu wahala.
Tace da zata samu Mijin aure, zata yi aure ta huta.
https://www.tiktok.com/@officielhassanmakeup227/video/7590881103548894476?_t=ZS-92l4dwPER04&_r=1
Direban motar da ta yi hadari da dan damben Najeriya, Anthony Joshua inda har abokansa 2 suka rasu yace da Anthony Joshua ne ya zauna a gaban motar.
Yace amma daga baya sai yace yana kare masa madubin gefe ya koma baya abokinsa ya dawo gaban motar.
Abokan Anthony Joshua biyu dai duka sun rasu a hadarin inda shi kuma ciwuka ba masu tsanani ba yaji.
Fasto Ayodele ya bayyana cewa, ko Tinubu ne zai zama shugaban INEC, ba zai ci zaben shekarar 2027 ba muddin ya dage akan sai ya karbi kudin Haraji a hannun 'yan Najeriya.
Ya bayyana hakane a cocinsa ga mabiyansa.
https://twitter.com/i/status/2007162007884313013
Hakan na zuwane yayin da shugaba Tinubu yace maganar karbar Haraji ba gudu ba ja da baya.
Rahotanni sun bayyana cewa, Wani Jirgi marar Matuki ya fadi a dajin jihar Naija.
Lamarin ya dauki hankula da saka fargaba a zukatan mutane.
Musamman ma saboda harin da kasar Amurka ta kawo Najeriya a jihar Sokoto a kwanakin baya.
Saidai sabbin bayanan da ake samu game da jirgin shine cewa, na sojojin saman Najeriya ne dake tattara bayanai daga Tshàgyèràn Dhàjì.
Me magana da yawun hukumar sojojin saman Najeriya, Air Commodore Ehimen Ejodame ya tabbatar da hakan.
Yace jirgin yana tattara bayanai ne daga Tshàgyèràn Dhàjì a yayin da ya fadi inda yace amma bai kashe kowa ba ko jikkata kowa ba.
Yace amma cikin hadin gwiwa da sauran abokan aikinsu, an dauko jirgin daga inda ya fadi.