Monday, December 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Isa Ƙasar Saudiyya Domin Gudanar Da Jana’izar Alhaji Aminu Ɗantata

Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Isa Ƙasar Saudiyya Domin Gudanar Da Jana’izar Alhaji Aminu Ɗantata

Duk Labarai
Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Isa Ƙasar Saudiyya Domin Gudanar Da Jana’izar Alhaji Aminu Ɗantata. Tawagar gwamnatin tarayya ta isa ƙasar Saudiyya domin gudanar da jana’izar fitaccen ɗan kasuwa, dattijo, Alhaji Aminu Ɗantata a birnin Madina, wanda ya rasu a ƙasar Dubai yana da kimanin shekaru 94 a Duniya, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito. Tawagar wadda ke ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Jihar Jigawa, kuma ministan tsaron ƙasa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, ta haɗa da ministan shari’a Lateef Fagbemi SAN, da ministan yaɗa labarai da wayar da kai, Alhaji Muhammad Idris, da ƙaramin ministan gidaje, Yusuf Abdullahi Ata. Sauran ƴan tawagar sun haɗa da: manyan malaman addinin musulunci, Dakta Bashir Aliyu Umar, Shaik Aminu Ibrahim Daurawa da kuma Khalifa Abdullahi Muhammad,...
Tonon Silili: Ji yanda shugaba Tinubu ya tafi neman lafiya a asirce dan kada ‘yan Najeriya su mai surutu

Tonon Silili: Ji yanda shugaba Tinubu ya tafi neman lafiya a asirce dan kada ‘yan Najeriya su mai surutu

Duk Labarai
Rahotanni sun ce tafiyar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi zuwa kasar Saint Lucia da fadar shugaban kasar tace hanyace ta kulla alaka tsakanin kasashen biyu, dabara ce kawai ta neman lafiya da shugaban kasar ya fita yi. Rahoton yace Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi amfani da kasar Saint Lucia ne dan neman magani inda maimakon a baya da yake zuwa asibiti, a wannan karin likitocin sa ne za'a dakko su dubashi a kasar. Rahoton wanda ya fito daga Sahara reporters wadda ita kuma tace ta samoshi ne daga wata majiya me tushe ta kusa da shugaban kasar tace, an yi hakanne dan kaucewa idon 'yan jarida kada su kwarmata cewa shugaban kasar ya je nema lafiyane. A baya dai shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya je neman lafiya kasashen waje wanda hakan yaci karo da suka daga 'yan Naje...
Da Duminsa: APC ta yi magana kan komawar Kwankwaso jam’iyyar

Da Duminsa: APC ta yi magana kan komawar Kwankwaso jam’iyyar

Duk Labarai
Jam'iyyar APC ta yi magana kan rade-radin dake jawo cewa Dr. Rabiu Musa Kwankwaso na shirin komawa jam'iyyar. Hakan na zuwane bayan da Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ajiye mukaminsa a matsayin shugaban jam'iyyar APC inda ake ta samun rahotannin cewa, yanzu Kwankwaso zai koma jam'iyyar. Me magana da yawun jam'iyyar APC a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV yace babu wannan maganar. Yace bai san komai ba game da rahotannin dake yawo cewa Kwankwaso zai koma jam'iyyar APC ba. A wasu rahotannin dai har cewa aka yi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai dauki Kwankwaso a matsayin abokin takararsa.
Ji yanda Matasan jihar Anambra ke soyayya harma da aure dan kawai su rika haihuwar jarirai suna sàyàrwà

Ji yanda Matasan jihar Anambra ke soyayya harma da aure dan kawai su rika haihuwar jarirai suna sàyàrwà

Duk Labarai
Hukumar yaki da safarar mutane ta Najeriya, NAPTIP tace matasan jihar Anambra sun baci da dabi'ar sayar da jarirai. Kwamandar hukumar ta jihar, Ibadin Judith-Chukwu ce ta bayyana hakana wata sanarwa data fitar inda tace abin yayi yawa tsakanin matasa. Tace abin yafi kamari a kauyuka dan hakane suka kafa wata tawaga ta musamman dan yaki da wannan mummunar dabi'a. Ibadin Judith-Chukwu tace matashi zai yiwa yarinya ciki dai ya aureta amma tana haihuwar jaririn sai ya lalaba ya saceshi ya sayar bada sanin mahaifiyar ba. Tace amma suna ta kokarin wayarwa da mutane kai game da lamarin.
Tinubu Rahama ne ga Najeriya, Ya hana mutane da yawa mutuwa>>Inji Kungiyar kare muradin Yarbawa ta YCG

Tinubu Rahama ne ga Najeriya, Ya hana mutane da yawa mutuwa>>Inji Kungiyar kare muradin Yarbawa ta YCG

Duk Labarai
Kungiyar kare muradun yarbawa ta YCG ta bayyana shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a matsayin shugaba na gari wanda rahama ne ga 'yan Najeriya. Kungiyar tace tsare-tsaren shugaba Tinubu sun taimaka wajan samar da tsaro, ga rayuwa da dukiyoyin jama'a. Kungiyar tace a cikin shekaru 2 da shugaba Tinubu yayi yana mulki, Gwamnatinsa ta samar da tsaro da kara karfin tattalin arzikin Najeriya. Wakilan Kungiyar Olugbemga Oyewusi, Mrs Buky Tunde Oshunrinde, ne suka bayyana hakan a sanarwar da suka fitar ga manema labarai. Sun ce Yabo Shugaba Tinubu ya cancanta ba barazana da zagi ba.
Gwamnan Kano ya jagoranci tawogar Kano da Jigawa zuwa halartar jana’izar Dantata a Madina

Gwamnan Kano ya jagoranci tawogar Kano da Jigawa zuwa halartar jana’izar Dantata a Madina

Duk Labarai
Gwamnan Kano ya jagoranci tawogar Kano da Jigawa zuwa halartar jana'izar Dantata a Madina. Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano, inda yake jagorantar wata babbar tawaga domin halartar jana’izar fitaccen attajiri kuma dattijon kasa, marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata, a birnin Madina mai alfarma, da ke Kasar Saudiyya. Marigayin ya rasu da safiyar Asabar a birnin Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa. Wannan bayanin na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar. Tawagar tana dauke da Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, tsohon gwamnan Jigawa Barr. Ali Sa’ad Birnin Kudu, da wasu manyan jami’an gwamnati da fitattun dattawa...
Kamfanonin Dangote sun zo na daya a Afrika wajan samar da kayan Masarufi a shekarar 2025

Kamfanonin Dangote sun zo na daya a Afrika wajan samar da kayan Masarufi a shekarar 2025

Duk Labarai
Kamfanonin Dangote ne suka zo na daya a Nahiyar Africa wajan samar da kayan Masarufi na yau da kullun a shekarar 2025. Kafar The African Exponent ce wadda ta shahara wajan samar da bayanan kasuwanci ta bayyana hakan. Face Dangote ya zo na daya da kamfanoninsa na Sugar, Gishiri, Taliya da Macaroni da sauransu. Kamfanin Nestlé dake yin Milo, Nescafé, Cerelac, da Maggi ne ya zo na biyu inda yake da rassa a kasashen Nigeria, Ghana, South Africa, da Côte d’Ivoire. Daga nan kuma sai kamfanin Unilever wanda ya zo na 3, shine ke yin OMO, Close-Up, Lipton, Vaseline, da magin Knorr. Kuma yana da rassa a kasashe kusa 20 na Afrika. Kamfanin Africa ta kudu me sunan Tiger Brands ne ya zo na 4. Sai kamfanin SABMiller AB InBev wanda shima na kasar Africa ta kudi ne ya zo na 5. Kamf...
Babu tsageran da ya fi karfin mu a kasarnan>>Inji Janar din Soja

Babu tsageran da ya fi karfin mu a kasarnan>>Inji Janar din Soja

Duk Labarai
Major General Ijioma Nwokoro Ijioma ya bayyana cewa, babu dan ta'addar da ya fi karfin sojojin Najeriya. Janar din me ritaya na daga cikin wadanda aka tura zuwa kasar Sudan dan kwantar da tarzoma a tsakanin shekarun 2013 zuwa 2015. Hakanan ya yaki kungiyar Bòkò Hàràm inda ya kwato karamar hukumar dake hannunsu. Janardin wanda akawa ritayar dole ya bayyana cewa matsalar Najeriya shugabanci ne kuma shiyasa shuwagabannin saboda sun san basu da nagarta sai su rika amfani da kabilanci da addini wajan neman nasarr cin zabe.
Ji sunayen Gwamnoni 5 da zasu koma APC saboda goyon bayan sake zaben shugaba Tinubu a 2027

Ji sunayen Gwamnoni 5 da zasu koma APC saboda goyon bayan sake zaben shugaba Tinubu a 2027

Duk Labarai
Jam'iyyar APC tace akwai karin Gwamnoni 5 da zasu koma jam'iyyar nan da watanni 2. Mataimakin shugaban jam'iyyar daga yankin kudu maso gabas, Dr Ijeoma Arodiogbu ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi dashi a jaridar Punchng. Ya bayyana cewa gwamnonin jihohin Bayelsa, Rivers, Plateau, Kano, da daya daga cikin gwamnonin Abia ko na Enugu ne zasu koma jam'iyyar APC. Yace wannan ba jita-jita bane, tabbas ne kuma nan da watanni 2 kowa zai tabbatar da hakan. Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga shugabancin jam'iyyar APC inda yace zai je ya kula da lafiyarsa.