Ji irin Wulakancin da Akawa Ganduje kamin ya sauka daga shugaban APC
Rahotanni sun tabbata cewa Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga shugaban APC.
Wasu bayanai sun ce kamin saukarsa Ganduje, an cire duk wasu kayan aikinsa daga ofishinsa dake hedikwatar jam'iyyar APC dake Abuja.
Rahoton yace kuma daga fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu aka umarci Ganduje ya sauka daga mukamin nasa.
Wane ne Abdullahi Ganduje?
An haifi Abdullahi Umar a ƙauyen Ganduje da ke cikin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kano a 1949.
Ya fara karatun Ƙur'ani da Islamiyya a ƙauyensu, inda ya samu ilimin addini. Ya shiga firamare ta Dawakin Tofa daga 1956 zuwa 1963.
Ganduje ya fara makarantar sakandiren Birnin Kudu a 1964 inda ya kammala a 1968.
Ya shiga makarantar horar da malamai da ke Kano tsakanin 1969 zuwa 1972.
Tsohon gwamnan jihar Kanon ya samu d...






