Za a fara sauya tunanin tubabbun ƴanbindigar da suka miƙa makamai a Katsina
Gwamnatin jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce za ta soma shirin sauya tunanin tubabbun ƴanbindigar da suka miƙa makamai nan bada jimawa ba.
Gwamnatin ta ce za a buɗe azuzuwan koyar da karatu da dubarun koyar da sana'o'i domin sauya tunanin ƴanbindigar, inda daga bisani za su koma cikin al'umma.
Hukumar da ke kula da ilimin manya ta jihar ce ke da alhakin tsara yadda shirin sauya tunanin tubabbun ƴanbindigar zai kasance.
Ƙarƙashin shirin za a bai wa waɗanda suka miƙa makamansu damar koyon karatun zamani da na addinin musulunci tare da fahimtar da su illar kisan mutane da kuma neman fansa.
Daraktar hukumar ilimin manya ta jihar Katsinan Bilkisu Muhammad Kakai, ta tabbatarwa da BBC wannan shiri da gwamnatin jihar zata fara.
Daraktar ta sanar da manema labarai...







